Buhari tubalin karamci ne a duniya - Onochie

Buhari tubalin karamci ne a duniya - Onochie

- An yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari kyakkyawan lakabi na kasancewa madubin haskaka karamcin Najeriya a idon duniya

- Hadimar shugaban kasa a kan sabuwar hanyar sadarwa, Lauretta Onochie, ita ta bayyana hakan a ranar Juma'a 15 ga watan Afrilu cikin shafin sada zumunta na facebook

- Lauretta ta na daya daga cikin tawagar shugaban kasa Buhari da ta ziyarci kasar Jordan

Cikin shafin sada zumunta na Facebook a ranar Juma'a 5 ga watan Afrilu, hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan sabuwar hanyar sadarwa, Lauretta Onochie, ta yi ma sa lakabi da madubi mai haskaka karamcin kasar Najeriya a idon duniya.

Tawagar shugaba Buhari yayin saukar ta a kasar Jordan

Tawagar shugaba Buhari yayin saukar ta a kasar Jordan
Source: Facebook

Lauretta na daya daga cikin tawagar shugaban kasa Buhari da ta ziyarci kasar Jordan in da aka gayyace shi domin gabatar da jawabai na bude taron tattalin arziki na duniya a Gabas ta Tsakiya da kuma Arewacin Afirka.

Kamar yadda Lauretta ta bayar da shaida, ana ci gaba da yi masu tarba da lale maraba a kasar Jordan cikin mafi kololuwar girmamawa a sanadiyar kasancewar su cikin tawagar shugaban kasa Buhari da ya zamto haske na karamci.

A cewar shugaban kasa Buhari, ya yi farin cikin matauka na samun karamcin gabatar da jawaban a babban taron na tattalin arziki duk da kasancewar Najeriya ba ta cikin jerin kasashen Gabas ta Tsakiya ko kuma Arewacin Afirka.

KARANTA KUMA: Osinbajo ya gana da tsohon Firai Ministan Birtaniya, Tony Blair

Lauretta yayin yabo da jinjina ga shugaban kasa Buhari, ta ce duniya ta aminta da shi a matsayin wani tubali kuma ginshiki mai haskaka karamcin kasar sa ta Najeriya da ko ina a fadin duniya ake mutuntata a sanadiyar sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel