Dr. Ahmad Gumi yayi magana a kan satar mutane da ake yi a Najeriya

Dr. Ahmad Gumi yayi magana a kan satar mutane da ake yi a Najeriya

Daily Trust ta rahoto cewa Fitaccen Malamin addinin Musulunci, Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi yayi magana a kan matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a halin yanzu a bangarorin Najeriya.

Babban Malamin na Musulunci na Najeriya ya koka da matsalar da aka shiga na satar Bayin Allah ana garkuwa da su. Shehin Malamin yake cewa wannan mugun aiki bai rasa nasaba da halin tattalin arzikin da Najeriya ta ke ciki a yau.

Ahmad Gumi ya bayyana cewa jami’an tsaro ba su yi abin da ya kamata wajen ganin sun kawo karshen wannan mugun lamari. Malamin yake cewa kudin da ake karba da nufin fansa idan aka yi garkuwa da mutane yana da ban tsaro.

KU KARANTA: Garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a wasu Jihohin Arewa

Dr. Ahmad Gumi yayi magana a kan satar mutane da ake yi a Najeriya

Sheikh Ahmad Gumi ya nemi a kawo karshen matsalar rashin tsaro
Source: Depositphotos

Sheikh Ahmad Gumi yake cewa a cikin ‘yan kwanakin nan ne aka sace wani mutumi da ya sani. Gumi yace yanzu ana neman Iyalin sa su kawo wasu mahaukatan kudi da ba su taba ganin irin su ba. Satar jama’an dai ya zama ruan dare.

Gumi yace abin da ake neman ‘Yan uwan wannan mutumi su kawo domin fansa ya haura Naira Miliyan 20, wannan ya sa babban Malamin nan Fikihun Musulunci yake ganin wannan musiba yana nema ya zama matsalar kowa a kasar.

Malamin yace dole a ajiye siyasa a gefe a zo a zauna idan har ana so a shawo ksrshen lamarin a huta. Ana fama da wannan matsala ne musamman a cikin jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya irin su Kaduna, Zamfara da kuma Katsina.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel