Gobara ta kama dakunnan 'yan NYSC a jihar Sokoto
- Gobara ta kama dakin 'yna bautar kasa a jihar Sokoto
- Gobarar ta kamadakin sanadiyyar haduwar wayoyin wutar lantarki
- Ba ayi asarar rai ba sai dai ta kone kayyakin wasu daga cikin masu bautar kasar dake dakin
Wata gobara ta kama dakunan 'yan bautar kasa dake karamar hukumar Wamakko cikin jihar Sokoto. Shugaban masu bautar kasar na jiha, Philip Enaberue, shine ya tabbatar da hakan, inda ya bayyana cewa lamarin ya faru a jiya Laraba da misalin karfe 7 na safe.
Bayan haka kuma shugaban ya bayyana cewa wutar ta shafi daki daya ne wanda ya ke dauke da 'yan bautar kasa guda 20.
Ya kuma bayyana cewa akwai yiwuwar wutar ta kama ne sanadiyyar hadewar wayar wutar lantarki, amma ya zuwa yanzu dai ana cigaba da gabatar da bincike, don gano dalilin kama wutar.
Ya ce wutar ta yi sanadiyyar kone kayan 'yan bautar kasa su biyar, sannan babu takardu ko wasu abubuwa masu muhimmanci da wutar ta kona.
KU KARANTA: A karo na farko Shugaba Buhari ya yi magana akan zaben Kano
Ya ce sojoji sun kashe gobarar tare da taimakon wasu daga cikin 'yan bautar kasar.
Yanzu haka dai an canjawa wadanda abun ya shafa daki, sannan an ba su kudi domin su saya kayyayakin da wutar ta kona musu, sannan kuma na sake ba su kayan bautar kasa sababbi.
A satin da ya gabata ne dai aka tura dalibai jihohi daban daban a kasar nan domin gabatar da bautar kasa, wanda yana daya daga cikin dokar kasar Najeriya, akan dole sai dalibin da ya gama jam'iyya ya yi kafin ya fara neman aikin yi a fadin kasar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng