Ambaliyar ruwa: Wata mata ta haihu a kan bishiyar mangoro

Ambaliyar ruwa: Wata mata ta haihu a kan bishiyar mangoro

Wata mata ta haihu a kan bishiyar mangoro yayin da tayi gudun neman mafaka bayan annobar ambaliyar ruwa da ake kira da 'Cyclone Idai' tayi awon gaba da muhallinsu a tsakiyar kasar Mozambique.

Matar mai suna Amelia ta haife diyar ta, Sara, yayin da take rike da reshen bishiyar a hannu guda, sannan tana rike da yaronta mai shekaru biyu a daya hannun.

Jama'a sun kai wa matar dauki bayan kwana biyu da afkuwar ambaliyar da tayi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 700.

A shekarar 2000, shekaru 20 da suka wuce, wata mata mai suna Rosita Mabuiango ta taba haihuwar diya mace a kan bishiya yayin gudun neman tsira sakamakon wata annobar ambaliya da ta faru a kudancin kasar Mozambique.

Ambaliyar ruwa: Wata mata ta haihu a kan bishiyar mangoro
Amelia da jaririyar ta
Asali: Twitter

"Ina cikin gida tare da yaro na mai shekaru biyu, sai kawai na ga ruwa ya fara kwararowa ba tare da na ankara ba.

DUBA WANNAN: Abinda yasa mambobin jam'iyyar suka ki zuwa karbar shaidar cin zabe a Kano - PDP

"Ba ni da wani zabi da ya wuce na fita na dare kan bishiya tare da yaro na," Amelia ta fada wa jami'in kungiyar asusun jin kan kanan yara ta duniya (UNICEF).

Yanzu haka Amelia da jaririyarta da ragowar iyalinta na zaman wucin gadi a wani gida dake kusa da Dombe, rahotanni sun ce suna cikin koshin lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel