Gwamnatin Buhari ta batar da N300bn wajen shirin tallafin jin dadin rayuwa

Gwamnatin Buhari ta batar da N300bn wajen shirin tallafin jin dadin rayuwa

Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo, ta batar da kimanin N300bn wajen shirye-shiryen tallafi na inganta jin dadin rayuwar musamman Matasa da kuma Mata.

Babbar mai bai wa shugaban kasa shawara ta musamman akan harkokin shirin tallafin inganta jin dadin rayuwa, Maryam Uwais, ita ce ta bayar da shaidar hakan cikin garin Abuja yayin wata ziyarar bude ido ta kwamitin Majalisar tarayya a kan yaye talauci.

Maryam Uwais

Maryam Uwais
Source: UGC

Sanata Lawal Gumau na majalisar dattawa da kuma na majalisar wakilai, Muhammad Wudil, su ne su ka jagoranci tawagar kwamitin su yayin kai ziyara kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Hajiya Maryam ta ce shirin tallafin na inganta jin dadin rayuwar Matasa da kuma Mata da gwamnatin shugaban kasa Buhari ta assassa tun a shekarar 2016, ya taimaka kwarai da aniyya a yayin da kimanin mutane miliyan 20 na al'ummar Najeriya ke cin moriyar sa.

Kazalika gwamnatin shugaba Buhari cikin shirin tallafin da ta assasa, ta na ciyar da kimanin mutane miliyan 9.5 na daliban Makarantun Firamare da Sakandire musamman a wasu yankuna na Arewa da suka afka cikin sarkakiya ta kuncin rayuwa.

KARANTA KUMA: Kowa ya aminta da sakamakon zaben gwamnan jihar Jigawa - Badaru

Cikin na sa jawaban, jagoran kwamitin kula da harkokin rangwami na talauci a majalisar wakilai, Muhammad Wudil, ya ce wannan ziyara ta bude ido za ta yi tasirin gaske wajen ganin gwamnatin kasar nan ta inganta shirin tallafi yayin shigar da kasafin kudin kasa na bana cikin doka.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel