Kowa ya aminta da sakamakon zaben gwamnan jihar Jigawa - Badaru

Kowa ya aminta da sakamakon zaben gwamnan jihar Jigawa - Badaru

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar, ya ce cikin dukkanin jihohin Najeriya ba bu inda aka gudanar da zabe cikin lumana da kwanciyar hankali tamkar yadda ta kasance yayin babban zabe a jihar Jigawa.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, gwamna Badaru ya bayyana hakan ne yayin karbar sakamakon babban zaben bana na 2019 da cibiyar yakin zabe ta Manpower Development Institute da gabatar a babban birnin jihar na Dutse.

Kowa ya aminta da sakamakon zaben gwamnan jihar Jigawa - Badaru
Kowa ya aminta da sakamakon zaben gwamnan jihar Jigawa - Badaru
Asali: Twitter

Gwamnan ya yi bayanin cewa, zaben jihar Jigawa tun daga mafarar sa zuwa karkewa ya gudana cikin mafi kololuwar lumana da kwanciyar hankali fiye da yadda ya gudanar cikin sauran jihohin da ke fadin Najeriya.

Yayin da dukkanin masu ruwa da tsaki su ka aminta da sakamako da kuma yanayi na gudanar zabe a jihar Jigawa, hukumomin kotu masu karbar korafin zabe sun koma yadda suka zo ba tare an shigar masu da wani kalubale ba.

KARANTA KUMA: Dangote ya shawarci Gwamnonin Arewa a kan yakar talauci

Gwamna Badaru ya ce wannan manuniya ce da ka haskaka yadda dukkanin 'yan adawa suka sallama tare da mika wuya wajen amintuwa da sakamakon zaben jihar da jam'iyyar APC ta mukurkushe sauran jam'iyyu.

Ya kara da cewa, jihar Jigawa ta kasance jiha daya tilo da kaso 55 cikin 100 na masu cancantar zabe suka fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri'un su cikin lumana da kuma kwanciyar hankali.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel