An shawarci zawarawa a jihar Jigawa su shiga kungiya

An shawarci zawarawa a jihar Jigawa su shiga kungiya

- Kungiyar zawarawa na jihar Jigawa tayi kira ga dukkan wadanda suka rabu da mazajensu suyi rajista da kungiyar

- Kungiyar ta ce muddin ba su hada kai wuri guda ba saboda su kasance suna magana da murya guda daya wurin magance matsalolin da ya shafe su

- Kungiyar ta kuma ce shiga kungiya itace hanya mafi sauki da zawarwan za su rika amfana da ayyuka da tsare-tsaren gwamnatin jihar

An shawarci zawarawa a jihar Jigawa su shiga kungiya
An shawarci zawarawa a jihar Jigawa su shiga kungiya
Asali: Twitter

Kungiyar zaurawa a jihar Jigawa ta fara wayar da kan matan da suka rabu da mazajensu a jihar su shigo kungiyar domin hada kai da sauran zaurawa da kuma magana da murya daya.

A lokacin da ta ke bayar da sanarwan a jiya Talata a karamar hukumar Buji, Shugaban kungiyar, Hadiza Suleiman ta ce ta ziyarci karamar hukumar ne domin ta tabbatar cewa dukkan zaurawan da ke jihar sun hada kai wuri guda domin su rika amfana da tsare-tsaren gwamnatin jihar.

DUBA WANNAN: Namadi Sambo ya goyi bayan Buhari kan tsare-tsaren sa na tattalin arziki

"Idan ba mu hada kan mu wuri guda ba, za a bar mu a baya. Wannna shine dalilin da ya sa muke wayar da kan dukkan zawarawa su shigo kungiyar mu domin su cimma burin mu tare.

"Idan bamu hada kai wuri guda ba, ko da gwamnati na son taimaka mana, ba za ta samu saukin aikata hakan ba. Wannan shine dalilin da ya sa muke tafiya sassan jihar muna wayar da kan zawarawa domin mu tabbatar sunyi rajitsa ta kungiyar mu," inji Hadiza Suleiman.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel