Ku kalli shugaban kasar da ya fi kowa talauci a Afirka

Ku kalli shugaban kasar da ya fi kowa talauci a Afirka

- Kyaftin Valentine Strasser ya yi juyin mulki a kasar Saliyo a shekarar 1992, in da ya yi ta nu na izza ta mulki, a karshe mataimakin sa ya hambarar shi

- A yanzu haka dai tsohon shugaban kasar ya zama abin tausayi, inda talauci ya sanya ko kudin magani ba ya iya biyawa kanshi

kyaftin Valentine Strasser shi ne wanda ya yi shugaban kasa mafi kankanta a Afirka ta Yamma, Kyaftin din ya hau mulki ta hanyar yin juyin mulki a shekarar 1992, a lokacin da ya ke da shekaru 25 a duniya, an tunbuke shi a shekarar 1996.

Strasser ya karbi mulki a kasar Saliyo, inda ya hambarar da tsohon shugaban kasar, Joseph Momoh, wanda mai gidansa ne a lokacin. A wancan lokacin Strasser, bayan wadata, yana kuma da ikon yin duk abinda ya ke so.

Ku kalli shugaban kasar da ya fi kowa talauci a Afirka
Ku kalli shugaban kasar da ya fi kowa talauci a Afirka
Asali: Facebook

Sai dai kuma a lokacin giyar mulki ta na juya shi, ya dinga amfani da karfin mulki yana abubuwan da ba su kamata ba, har ya kai matsayin da mutanen kasar ba sa kaunar shi, ya yi ta almubazzaranci da dukiyar kasar, wacce ya kamata ace anyi amfani da ita wurin kawo cigaba ga kasar.

A lokacin duk mutumin da ya yi kokarin nu na masa tawaye, Strasser ya kan saka a kashe shi. Da yawa daga cikin dakarun sa sun koma kungiyar 'yan tawaye, wanda suka samu rinjaye a kan shi gabanin hambarar da mulkinsa.

A karshe dai mataimakinsa, Julius Maada Bio, shi ne ya hambarar da mulkin Strasser a shekarar 1996.

KU KARANTA: San barka: Wani dan siyasa kuma mashahurin dan kasuwa, ya sauke Al-Qur'ani mai girma

A kokarin da ya yi na fara sabuwar rayuwa tsohon shugaban kasar ya gudu zuwa birnin Landan.

A cewar jaridar Flawlessview, tsohon shugaban kasar ya yi kokarin fara karatu a jami'ar Warwick, sai dai hakan bai yiwu ba, saboda rashin kudi da wurin kwana. A karshe kasar ta Saliyo ta dawo dashi gida inda ya je ya cigaba da zama da mahaifiyar shi.

Rahotanni sun nuna cewa tsohon shugaban kasar ya kamu da ciwon kafa, inda a yanzu haka ya ke kwance a asibitin Aspen da ke birnin Freetown.

Ku kalli shugaban kasar da ya fi kowa talauci a Afirka
Ku kalli shugaban kasar da ya fi kowa talauci a Afirka
Asali: Depositphotos

Bio wanda ya bar mulki a shekarar 1996, ya kara lashe zabe a matsayin shugaban kasa na biyar na mulkin demokaradiyya a shekarar 2018, rahotanni sun nuna cewa shugaban kasar ya kawo wa tsohon shugaban na shi dauki, inda ya ce zai yi iya bakin kokarin shi wurin nema masa lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel