Rayuka hudu sun salwanta a sabon rikicin kabilanci a jihar Taraba

Rayuka hudu sun salwanta a sabon rikicin kabilanci a jihar Taraba

A kalla mutane hudu ne suka rasa ransu yayin da aka kona gidaje da dama a wani sabon rikicin kabilanci da ya barke a tsakanin kabilun Jukun da Tiv a karamar hukumar Wukari da ke jihar Taraba.

Sai dai, kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya ce ba zai iya tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ba saboda rashin samun damar jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Taraba, Mista David Misal.

Amma wani shaidar gani da ido mai suna Jerry Luka ya shaida wa NAN cewar rikicin ya barke ne a ranar Litinin bayan wani sabani da ya shiga tsakanin kabilun a kauyen Kente.

"Sabani ne silar barkewar rikicin da ya jawo mutuwar wasu mutane biyu a kauyen Kante da kuma karin wasu mutane biyun a yankin babban asibitin garin Wukari.

"Sa-insa a kan batun gado ne ta jawo kabilun biyu ke rigima da juna tun ba yau ba," a cewar Luka.

Rayuka hudu sun salwanta a sabon rikicin kabilanci a jihar Taraba
Wukari
Asali: Facebook

Shugaban karamar hukumar Wukari, Mista Daniel Adi, ya tabbatar da faruwar rikicin, ya bayyana cewar mutum biyu sun mutu, an kona gidaje da dama.

A nasa bangaren, shugaban karamar hukumar ya ce rikicin ya barke ne sakamakon hana wasu 'yan kabilar Tiv shiga da kayan sana'arsu cikin kasuwar Kante.

"Wata mata guda daya ta ki yin biyayya da umarnin hana 'yan kabilar Tiv shiga kasuwar, kasa doyar sayar wa da ta yi ne ya jawo rikicin da har kabilar da ta fito suka kai kai harin daukan fansa.

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa tayi magana a kan kisan 'yar Najeriya a kasar Saudiyya

"Na samu tattauna wa da shugaban karamar hukumar Ukum da ke jihar Benuwe da kuma mai taimaka wa gwamnan jihar a kan harkokin tsaro, kuma muna iya bakin kokarin mu domin dakile yaduwar rikicin.

"Da ni da shugaban karamar Ukum mun ziyarci wurin da rikicin ya fara, kuma mun dauki alkawarin tsawatar wa da jama'ar mu domin a samu zaman lafiya," a cewar shugaban karamar hukumar.

NAN ta rawaito cewar barkewar rikicin ta jawo tsayawar harkokin kasuwanci a kasuwar doya ta Wukari saboda yawan dukiyar da aka lalata bayan 'yan kasuwar sun gudu domin neman mafaka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel