Fadar shugaban kasa tayi magana a kan kisan 'yar Najeriya a kasar Saudiyya
Gwamnatin tarayya ta bayyana kisan wata 'yar Najeriya da hukumomin kasar Saudiyya su ka yi da cewar abin haushi da bakin ciki da ban tausayi ne.
Ma'aikatar cikin gida a kasar Saudiyya ta bayyana cewar ta kashe wasu mutane uku; dan kasar Pakistan, dan kasar Yemen da wata mata 'yar Najeriya bayan samun su da laifin safarar kwaya zuwa cikin kasar. Kisan ya kawo adadin mutanen da hukumomi su ka kashe a wannan shekara zuwa mutum 53.
Da take magana da manema labarai a fadar shugaban kasa, Abike Dabiri-Erewa, mai taimaka wa shugaba Buhari a kan harkokin kasashen waje, matar da aka kashe ita ce cikon mutum na 9 'yan Najeriya da hukumomin suka kashe a kan laifin safarar kwaya a cikin shekaru uku.
Ta ce, yanzu haka akwai wasu 'yan Najeriya 20 da ke kan hanyar fuskantar irin wannan hukunci a kan laifin safarar kwaya, 12 kuma an yanke masu hukuncin zaman gidan yari a sassan kasar.
Dabiri-Erewa ta ce akwai ma'aikatan kamfanin jiragen sama da ke saka kwayoyi a jakar maniyyata aikin Hajji zuwa kasar Saudiyya.
A cewar ta, "wasu daga cikinsu basu aikata laifin da ake zarginsu da shi ba. Mun sha rokon hukumomin kasar Saudiyya a kan su ke gudanar da shari'ar irin wadannan mutane a bayyane domin tabbatar da adalci. Koda za a kashe mutum, zai fi dacewa ya san an kashe shi ne a kan laifin da ya aikata.
DUBA WANNAN: Hukumar NIS tayi karin girma ga manyan jami'ai 14
"Muna yin kira ga 'yan Najeriya da zasu ziyarci kasar Saudiyya, da su zamu masu biyayya ga dokokin kasar. Hatta goro suna bayyana shi a matsayin kwaya. Zamu cigaba da rokon hukumomin kasar Saudiyya da su zama masu sassauci."
Sannan ta kara da cewa hukumar jin dadin alhaxai ta kasa (NAHCOM) na cigaba da daukan matakai domin ganin ma'aikatan jiragen sama basu cigaba da jefa 'yan Najeriya cikin hatsari ba
Kazalika, hadimar ta shugabn kasa ta bayyana kamun da aka yiwa wasu 'yan Najeriya 5 a kasar Dubai da laifin fashi da makami a matsayin abin kunya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng