Masu garkuwa da Mutane sun yashe Mutane 8 a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Masu garkuwa da Mutane sun yashe Mutane 8 a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Ba don haka akan so ba mun samu rahoton cewa, da tsakar ranar Talata masu garkuwa da Mutane sun sake cin Kasuwa a kan hanyar birnin Abuja zuwa Kaduna yayin da suka tasa keyar Matafiya takwas rike da bindigu.

Mummunan lamarin ya auku ne bayan makamancin sa ya auku a ranar Litinin, inda azal ta masu garkuwa da Mutane ta afkawa kimanin Matafiya 37 a wani kauye da ke mararrabar birnin Abuja da Kaduna.

Masu garkuwa da Mutane sun yashe Mutane 8 a hanyar Abuja zuwa Kaduna
Masu garkuwa da Mutane sun yashe Mutane 8 a hanyar Abuja zuwa Kaduna
Asali: Twitter

Wani mashaidin wannan mugun ji da mugun gani ya shaidawa manema labarai na jaridar Daily Nigerian cewa, masu ta'adar sun ci karen su ba bu babbaka yayin ribatar makamai na bindigu wajen datse hanyar wasu Motoci biyu kirar Honda da kuma Toyota da misalin karfe 3.15 na rana.

Mashadin wanda mazauni ne a kauyen Akilibu, Lawan Sule, ya zayyana yadda masu ta'adar suka tasa keyar Matafiya takwas cikin dokar daji bayan sun katse masu hanzari ta hanyar harba harsashin bindiga a saman iska.

Kazalika masu garkuwa da Mutane sun ci karen su ba bu babbaka daura da kauyen Gidan Busa da ke da tazara ta kimanin Kilomita arba'in zuwa cikin garin Kaduna inda suka yi awon gaba da Matafiya 37 kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

KARANTA KUMA: Rashin tsaro a Najeriya ya na kuntata min - Aisha Buhari

A sanadiyar ci gaba da aukuwar wannan mummunan lamari, gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i, ya bayar da umarni ga 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro wajen tsananta tsaro a manyan hanyoyi na shigowa da kuma fita daga garin Kaduna.

Babban hadimi na musammann a fadar gwamnatin Kaduna, Samuel Aruwan, shi ne ya bayar da shaidar hakan bayan zaman majalisar tsaro na jihar da aka gudanar a ranar Talata musamman dangane da ta'adar da ke aukuwa a hanyar garin Birnin Gwari.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel