Najeriya na daya daga cikin kasashen da ba a bin su bashi sosai a duniya - Osinbajo

Najeriya na daya daga cikin kasashen da ba a bin su bashi sosai a duniya - Osinbajo

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa Najeriya ta na daya daga cikin kasashen da ba a bin su bashi da yawa a duniya

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce yanzu haka Najeriya ce kasar da ake binta bashi mafi karanci a duniya.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan, a lokacin da ya ke bayani a wani taro da ya halarta a jami'ar Lagos da ke Akoka, jiya 1 ga watan Afrilu.

Najeriya ta shiga jerin kasashen da ba a bin su bashi sosai a duniya
Najeriya ta shiga jerin kasashen da ba a bin su bashi sosai a duniya
Asali: Facebook

A lokacin da ya ke bayanin, mataimakin shugaban kasar ya ce gwamnatin shugaba Buhari ta yi kokari kwarai da gaske wurin farfado da tattalin arzikin Najeriya, a shekaru hudun da suka gabata.

KU KARANTA: A karo na farko Shugaba Buhari ya yi magana akan zaben Kano

"Mun yi iya bakin kokarin mu wurin ganin mun farfado da tattalin arzikin kasar nan, kuma hakan ta faru, saboda a halin yanzu cikin kashi 100 bai fi kashi 22 ake bin Najeriya ba, inda a yanzu bashin Najeriya ya na daya daga cikin mafi karancin bashi da ake bin kasashen duniya," in ji Osinbajo.

Sai dai kuma a dai-dai lokacin da mataimakin shugaban kasar ya ke bayanin ba a bin kasar bashi da yawa, dunbin al'ummar kasar na zaune cikin talauci da yunwa.

A shekarun da suka gabata dai kasar Najeriya ta shiga wani hali na matsalar tattalin arziki, sanadiyyar faduwar danyen man fetur a kasuwannin duniya, wanda a lokacin shi ne babban abin da kasar ta ke dogaro da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel