Jan hankali: Hukumar NAFDAC na jawo hankalin al'umma akan wani maganin bogi da ya ke yawo cikin al'umma
A wani jan hankali da hukumar NAFDAC ta ke ta gargadi al'umma akan wani sabon magani na bogi da ya fito wanda zai iya yiwa mutane illa matuka
hukumar NAFDAC ta gargadi al'ummah, musamman ma wadanda ke fannin lafiya, akan shigowar wani maganin bogi na cutar amai da gudawa, mai suna Dukoral Oral Cholera Vaccine, wanda a yanzu haka yana nan yana yawo a kasar Bangaladash.
A sanarwar da darakta janar na hukumar ya fitar, Farfesa Moji Adeyeye, ya ce a jikin kwalin maganin bogin akwai rubutu da aka yi shi da turanci da kuma na faransanci.
Adeyeye ya ce hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta kwace irin maganin da yawa a hannun mutane.
"Muna sanar da hukumomin lafiya da kuma al'umma akan fitowar wani maganin amai da gudawa na bogi, wanda yanzu haka ya ke yawo a kasar Bangaladash.
"Ofishin hukumar lafiya ta duniya da ke kasar Bangaladash ta samu damar kwace kwalaye 8,000 na maganin.
"Bayani dangane da maganin bogin shine kamar haka - Sunan maganin da turanci Dukoral Oral Cholera Vaccine, in da aka fassara shi da yaren faransanci da Vaccin Oral contre le Cholera, lambar maganin KV8262B1, lokacin da maganin zai lalace 2020-04, sannan an yi maganin Valneva kasar Canada.
"Ya kara da cewa kuma akwai hoton kamfanin a jikin kwalin,"
KU KARANTA: Kotu ta sa a kamo Nnamdi Kanu a duk inda ya ke
Shugaban hukumar NAFDAC din ya bayyana cewa kamfanin na gaskiya da ya ke buga maganin sunan sa Dukoral Oral Cholera Vaccine, sai dai shi kuma kamfanin yana kasar Sweden ne, wanda aka fi sani da Sweden AB.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng