San barka: Wani dan siyasa kuma mashahurin dan kasuwa, ya sauke Al-Qur'ani mai girma

San barka: Wani dan siyasa kuma mashahurin dan kasuwa, ya sauke Al-Qur'ani mai girma

Wani mashahurin dan siyasa, kuma dan kasuwa, ya yi abinda ba dukkanin 'yan siyasa su ke iya yin shi ba, duk da shekaru, hidimomi, da iyali, amma bai sanya ya koma gida ya kwanta ba, sai da ya fita neman ilimin addini

A wata walima mai ban sha'awa, da aka gabatar ranar Asabar dinnan 30 ga watan Maris, a gidan mashahurin dan siyasa, kuma shahararren dan kasuwa, Alhaji Bala Bello Tinka.

Gidan attajirin ya cika da mutane, wadanda su ka hada da 'yan uwa da abokanan arziki, domin ta ya shi murnar kammala saukar Al-Qur'ani mai girma a lokacin da ya ke da shekaru 51 a duniya.

Bayan Alhaji Bala Tinka, akwai abokanan sa guda shida, wadanda suka samu damar kammala karatun Al-Qur'anin tare, karatun da suka samu damar kammalawa a cikin shekara hudu.

San barka: Wani dan siyasa kuma mashahurin dan kasuwa, ya sauke Al-Qur'ani mai girma
San barka: Wani dan siyasa kuma mashahurin dan kasuwa, ya sauke Al-Qur'ani mai girma
Asali: Twitter

Abokanan na sa sun hada da; Sadisu Magaji, mai shekaru 50; Aminu Ahmed, mai shekaru 48; Ahmad Abdulkadir Tsada, mai shekaru 56; Muhammad Maigana, mai shekaru 58; Injiniya Mohammed Musa da kuma karamin cikinsu, Muhammad Abba Pantami, mai shekaru 39.

Bakin da su ka halarci taron sun yi wa mutanen fatan alkhairi, sannan kuma sun yi musu jinjina da irin namijin kokarin da suka yi wurin ganin sun sauke littafi mai tsarki, duk da irin harkoki da su ke da su na yau da kullum.

Tinka da abokanan na sa sun fara karatun Al-Qur'anin shekaru hudu da suka wuce, a wurin Malam Dahir Al'amin.

KU KARANTA: Kotu ta sa a kamo Nnamdi Kanu a duk inda ya ke

Malamin ya ce: "Mun fara karatun shekaru hudu da suka wuce a lokacin da suka neme ni na dinga koyar da su Al-Qur'anin. A lokacin da mu ka fara wasu daga cikinsu ko kalmar larabcin ma ba sa iya karantawa, amma cikin ikon Allah da kuma jajircewarsu, yanzu sun kammala sauke Al-Qur'anin duka."

Wani abun ban sha'awa kuma game da mutanen, duk da su suna da aure da iyali, sai gashi kuma malamin na su saurayi ne dan shekara 26.

Malamin ya ce: "Lokacin da muka fara karatun ina da shekaru 22 a duniya, amma duk cikin su ba bu wanda ya ta ba nu na min cewar ni yaro ne, kuma suna bani girma kamar yanda dalibai wadanda ba su kaini shekaru ba su ke yi," in ji malamin.

A bayanin da ya yi, Bala Tinka, wanda shi ne ya hada walimar ya ce, sun shirya walimar ne ba wai don ayi biki a tashi ba, sai don ba wa mutane kwarin guiwa, akan so fita neman ilimin addini.

Walimar wacce ta samu halartar manyan malamai irin su Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, shugaban kungiyar Izala na jiha, Sheikh Hamza Adamu Abdulhamid, Sheikh Adamu Girbo, Sheikh Usman Isa Taliyawa, Dr Nazif Muhammad Inuwa, Usman Baba Liman (Rtd), kwamishinan zakka na jihar Kano, da kuma 'yan siyasa da manyan 'yan kasuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel