'Tun ina 'yar shekara 8 mahaifina ke kwanciya da ni'
A wata hira da ta yi da manema labarai, yarinyar ta bayyana 'yadda mahaifinta ya dinga cin zarafinta, ya na amfani da ita, sannan ya na daukar ta ya na kai ta wurin wasu don ayi amfani da ita a ba shi kudi
Ga yadda hirar ta kaya da yarinyar:
"Na tashi a wani gida wanda ake rikici kuma mahaifina ya na cin zarafina. Ina shekara takwas ya fara yi mini fyade, a nan ne ya fara shirya yin amfani da ni daga baya. Ina shekara 11 ya sayar da ni domin a ringa yin jima'i da ni.
"Ina da kanwa amma ita ba haka mahaifin namu ya ringa yi mata ba. Mahaifina ya yi mini barazanar cewa idan na fada wa wani jikina zai gaya min, wannan shi ne dalilin da ya sa na yi shiru. A makaranta ina zuwa wajen likita."
"Zan fita tare da kawayena. Ina fita wurin wasan gudu, a kowanne karshen mako, amma ba bu wanda ya san abin da ke faruwa da ni, kawai dai na cigaba da rayuwa a hakan.
"A lokuta da dama mahaifina ya na kai ni gidajen wasu mutane. Wasu lokutan muna kwana a gidan mutanen, sai ya ce wa mahaifiyata a can zan kwana, wasu lokutan mahaifina zai aje ni inda ya ke dauka ta. Zai cire mini kaya na ya fita dani, sai mutumin ya gama amfani dani, sannan zai dawo daga baya ya kawo mini kaya na sai mu tafi gida.
"An yi amfani da ni a wurin ajiye kaya tare da wasu matan, masu neman suna da yawa akwai wata mata wadda ke bayar da mu ga masu amfani da mu."
KU KARANTA: Kotu ta sa a kamo Nnamdi Kanu a duk inda ya ke
"Yadda mahaifina ya tarbiyantar da ni ya sauya komai, ya sauya ni sosai. Ya sanya ni na ji kamar komai yayi daidai ne"
"A lokacin da nake shekara 28, ba ni da waya amma ina iya amfani da na'ura mai kwakwalwa. A lokacin ne na ga wannan kungiyar da za ta iya taimaka mini sai na yi musu magana sai suka zo washe gari inda suka dauke ni, suka fita da ni daga jihar da muke suka kai ni wani wuri mai kyau.
"Ga duk wanda ake safararsu, wannan mataki ne mai tsauri yana da wuya ka fita daga lamarin. Amma hakan shine abu mai kyau da ya dace. Za ka gaya wa wani. Akwai wahala warkewa. Amma idan ka fara kokartawa, hakan ya fi. Kuma hakan shi ne zai bawa mutum damar samun rayuwa mai inganci," in ji yarinyar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng