INEC ta fara shirin rage adadin jam'iyyun siyasa na Najeriya

INEC ta fara shirin rage adadin jam'iyyun siyasa na Najeriya

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC, ta bayyana damuwa dangane da yadda adadi na yawan jam'iyyun siyasa a kasar nan ke ci gaba da hauhawa da a halin yanzu ya ke damalmala mata lissafi yayin zabe.

INEC ta ce ta na da ikon watsar da wasu jam'iyyu da suka gaza cika sharudda da kuma tanadin tsari da aka shimfida cikin kundin tsarin mulkin kasar nan. Hukumar ta yi kira da gudanar da zaman shawarwari domin dinke wannan baraka.

Yayin zaman tuntube-tuntube da shawarwari, INEC ta yi kira da a yi baja koli na dalilai dangane na yiwuwar ci gaba da tabbatuwar fiye da jam'iyyun siyasa 100 a fadin kasar nan domin fafatawa yayin zabukan kasa.

Shugaban hukumar INEC na kasa; Farfesa Mahmood Yakubu
Shugaban hukumar INEC na kasa; Farfesa Mahmood Yakubu
Asali: Twitter

Kwamishinan sadarwa na hukumar INEC, Festus Okoye, shi ne ya yi wannan tsokaci cikin jawaban sa yayin mallakawa gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, takardun shaidar kasancewa zababben gwamnan jihar, Mataimakin sa da kuma 'yan majalisun dokoki na jihar.

Okoye cikin jawaban da ya gabatar yayin ganawa da manema labarai a birnin Makurdi na jihar Benuwe, ya kuma yi furuci na bayar da hujjoji gami da dalilai na gudanar da zaben cike gurbi a Najeriya.

KARANTA KUMA: Za mu fadada shirin N-Power - Osinbajo

Babban jami'in na hukumar INEC ya kuma yi kira na neman hadin gwiwar dukkanin masu ruwa da tsaki akan goyon bayan kare martabar kasar nan musamman ta hanyar ci gaba da tabbatuwar kwararar romon dimokuradiyya.

Okoye ya kuma kalubalanci kafofin sadarwa da su sanya idanun lura kan wasu jam'iyyun siyasa domin bankado ire-iren miyagun ababe da suke aikatawa yayin musamman a lokuta na kakar zabe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng