Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Mutane 4 yan gida daya sun mutu a hadari a Bauchi

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Mutane 4 yan gida daya sun mutu a hadari a Bauchi

Mutane goma sha uku sun rigamu gidan gaskiya a sakamakon wani mummunan hadarin mota daya rutsa dasu a akan babbar hanyar Gombe zuwa Bauchi, daga cikinsu akwai mutane hudu yan gida daua, da suka hada da Miji, matarsa da yaya biyu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya auku ne a ranar Lahadi, 31 ga watan Maris, yayin da Magidancin mai suna Jamal Yari tare da matarsa Amina, kanwarsa Zahra’u, da yayansa guda biyu Affan da Adnan suke dawowa daga jahar Gombe zuwa Bauchi a cikin motarsa kirar Camry.

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Mutane 4 yan gida daya sun mutu a hadari a Bauchi
Iyalan
Asali: UGC

KU KARANTA: An jefi Gwamnan Jihar Kano Ganduje da Tawagarsa a Goron Dutse

Lamarin ya faru ne a daidai kauyen Bishi, inda motar Jamal tayi taho mu gama da wata babar mota, yayin da dukkaninsu suke tsananin gudu, sai dai ba tare da bata lokaci ba aka yi musu jana’iza a fadar sarkin Bauchi.

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Mutane 4 yan gida daya sun mutu a hadari a Bauchi
Hadari
Asali: UGC

Sai dai an garzaya da sauran mutane shida da suka samu munanan rauni a sanadiyyar hatsarin zuwa babban asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dage garin Bauchi, inda suke samun kulawa.

Da yake tabbatar da lamarin, kaakakin rundunar Yansandan jahar, DSP Kamal Datti Abubakar ya bayyana cewa motoci biyu ne suka yi taho mu gama akan titin Gombe zuwa Bauchi, da suka hada da Sharon motar haya da Camry.

Daga nan muna taya iyalan mamatan alhinin wannan babban rashi, tare da fatan Allah Ya jikansu da gafara, Ya kuma baiwa iyalansu hakurin rashi, Amin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel