Rashin adalci a aikin dan sanda da siyasa: Na yi gudun gara na tarar da zago - Sanata Misau

Rashin adalci a aikin dan sanda da siyasa: Na yi gudun gara na tarar da zago - Sanata Misau

Sanata Isa Hamma Misau, shugaban kwamitin majalisar dattijai a kan harkokin sojojin ruwa (Navy), wanda ya yi suna saboda rikicin sa da tsohon shugaban rundunar 'yan sanda na kasa (IGP), ibrahim Idris, ya bayyana yadda ya fuskanci rashin adalci a siyasa bayan ya yi gudun hakan a aikin dan sanda.

A wata hira da aka yi da shi a kan zabukan shekarar 2019 da aka kammala da kuma harkokin siyasa, Sanata Misau ya yi bayani a kan dalilin sa na goyon bayan Bukola Saraki, shugaban majalisar dattijai

Da aka tambayi Sanata Misau ko da me 'yan Najeriya zasu tuna shi tunda bai samu damar komawa majalisa ba, sai ya amsa da cewar, "nima ban san da me 'yan Najeriya zasu ke tuna ni da shi ba.

"Ni dai na san na bayar da gudunmawa ta iya bakin gwargwado. Ban taba ganin baki na kira shi fari ba, ko naga fari na kira shi baki ba, saboda irin tarbiyar da na taso da ita da kuma horon aikin tsaro da na ke da shi.

Rashin adalci a aikin dan sanda da siyasa: Na yi gudun gara na tarar da zago - Sanata Misau
Sanata Misau
Asali: Twitter

"Hakan ne yasa na bawa Saraki goyon baya 100% bisa 100% a lokacin da naga gwamnati na kokarin yi masa rashin adalci, kuma bana nadamar yin hakan.

DUBA WANNAN: Zargin magudi: Za mu karbi kujerar mu a Kotu - APC ta fada wa Tambuwal

"Ban damu ba a kan rashin komawa ta majlisa. Na bar aikin dan sanda ne saboda rashin adalcin da aka nuna min, na shiga siyasa da tunanin zan kawo gyara a kan irin rashin adalcin da na gani a baya amma sai naga ita ma siyasar cike take da rashin adalci; akwai rashin adalci a tattare da harkokin Najeriya.

"Allah ne ke bayar da mulki, a saboda haka ban yarda cewar wani mutum ne silar faduwa ta zabe ba, ban damu ba kuma ina cikin farin ciki duk da na fadi zabe."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel