Dakarun Sojin Najeriya sun kashe Kwamandan Boko Haram da Mayakan sa 15 a Tafkin Chadi

Dakarun Sojin Najeriya sun kashe Kwamandan Boko Haram da Mayakan sa 15 a Tafkin Chadi

Rundunar kungiyar hadin gwiwar Dakarun sa kai ta Multinational Joint Task Force, MNJTF, ta samu nasarar kashe wani Kwamandan kungiyar masu tayar da kayar baya na Boko Haram tare da mabiyan sa 15 a gabar tafkin Chadi.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Dakarun masu fafutikar kare martabar kasar nan sun samu wannan gagarumar nasara da cin galaba akan mayakan Boko Haram yayin wani simame sharar daji da suka kai gabar Tafkin Chadi da ke iyaka da kasar Najeriya.

Dakarun Sojin Najeriya sun kashe Kwamandan Boko Haram da Mayakan sa 15 a Tafkin Chadi
Dakarun Sojin Najeriya sun kashe Kwamandan Boko Haram da Mayakan sa 15 a Tafkin Chadi
Asali: Facebook

Cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, kakakin rundunar MNJTF, Timothy Antigha ya bayyana cewa, ba ya ga kisan bazata, dakaru sun samu nasarar yin dugu-dugu da wasu Motocin yaki biyar mallakin 'yan ta'adda yayin da suka tari numfashin su ba tare da sun farga ba.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, dakarun MNJTF sun samu nasarar cafke wata Mata da kawowa yanzu ba bu masaniyar alakar da ke tsakanin ta da su.

KARANTA KUMA: Najeriya ce kasa ta 6 cikin jerin kasashen duniya mafi tabarbarewar tattalin arziki

Kanal Antigha ya ce, Kwamandan Mayakan Boko Haram mai rike da akala ta gudanarwar yankunan Daban Masara, Kirta Wulgo da kuma Koleram, Moussa mai ido daya, ya gamu da ajalin sa ba bu shiri.

Marigayi Moussa ya shahara wajen karbar haraji da kuma tara mai girman gaske kan Manoma, Masunta da kuma Makiyaya domin samun abin dogaro wajen dabbaka manufar su ta ta'addanci a yankin.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel