Hon. Baba da wasu su na marawa Aliyu-Betara baya a takarar kujerar Majalisa

Hon. Baba da wasu su na marawa Aliyu-Betara baya a takarar kujerar Majalisa

- Ana cigaba da kai da komowa a game da wanda zai rike Majalisar Tarayya ta 9

- Wasu ‘Yan Majalisar Wakilai sun matsawa Muktar Aliyu-Betara ya fito takara

- Honarabul Aliyu-Betara na APC shi ne ke wakiltar Biu/Bayo/Shani/Kwaya Kusar

Hon. Baba da wasu su na marawa Aliyu-Betara baya a takarar kujerar Majalisa
Wasu 'Yan Majalisa sun nuna goyon baya ga Aliyu-Betara na Borno
Asali: Twitter

Labari ya zo mana cewa wasu ‘Yan majalisa sun dage wajen ganin Mukhtar Aliyu-Betara wanda ke wakiltar Mazabar Biu/Bayo/Shani/da kuma yankin Kwaya Kusar ya fito takarar shugaban majalisar wakilai a wannan karo.

‘Yan majalisar tarayyar irin su Honarabul Ibrahim Baba na jam’iyyar APC su na marawa Takwaran na su na jihar Borno baya wajen ganin ya zama shugaban majalisar wakilan kasar a majalisar nan ta 9 da za a kafa a farkon Watan Yuni.

KU KARANTA: Mutane su na so su san nawa ‘Yan Majalisa su ke kashewa a duk shekara

Ibrahim Baba mai wakiltar Mutanen Katagum a jihar Bauchi da wasu ‘Yan uwan sa su na ganin cewa Ho.n Aliyu-Betara ya cancanci ya rike wannan babbar kujera a Najeriya. Yanzu haka dai akwai mutum 10 da ke neman kujerar.

Hon. Ibrahim Baba yace jama’a sun yaba da irin aikin da Aliyu-Betara yayi a kwamitin da ke lura da harkar tsaro a Najeriya don haka yake ganin za a amfana da irin kokarin sa da sanin aiki, idan har ya gaji Yakubu Dogara a bana.

Nan da watanni 2 ne za a kafa wata sabuwar majalisa don haka wasu ke ganin cewa Aliyu-Betara wanda yake majalisar wakilai tun 2007 yana cikin wadanda su ka fi dacewa. APC dai ta nuna cewa tana tare ne da Hon. Femi Gbajabiamila.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel