Tashin hankali: Yadda wani ya hau kololuwar karfen sabis ya fado kasa a Ibadan

Tashin hankali: Yadda wani ya hau kololuwar karfen sabis ya fado kasa a Ibadan

Wani bawan Allah da ba a bayyana sunansa ba ya hau kololuwar karfen sabis na bankin Wema da ke Eluwure junction a kan layin Sango-UI a garin Ibadan kuma ya daka tsalle ya fado ya mutu nan take.

Wani shaidan ido mai suna Tosin Alabi ya bayar da labarin yadda lamarin ya faru. "Ya shigo harabar bankin ta baya ne kuma ya hau can saman kololuwar karfen sabis din. Ya kwashe misalin mintuna 30 kafin ya daka tsalle ya fado a rufin bankin."

Daya daga cikin abokan mamacin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce abokinsa ba mahaukaci bane kamar yadda wasu mutane ke tsamani, ya kara da cewa marigayin abokinsa ne na kut da kut kuma akwai alamar tambaya a kan abinda ya faru dashi.

DUBA WANNAN: Buhari ya fadi dalilinsa na yin sallar Juma'a a masallacin fadar shugaban kasa

Wani mutum ya hau kololuwar karfen sabis ya daka tsalle ya kashe kansa
Wani mutum ya hau kololuwar karfen sabis ya daka tsalle ya kashe kansa
Asali: Twitter

Mahaifiyar marigayin, Mrs Alaba ta ce yaron ta bashi da tabin hankali inda ta kara da cewa duk abinda ya sanya ya kashe shi ba kankanin abu bane.

"Mun dawo daga addu'o'in dare kuma kammala karya kummalo, sai muka fara nemansa ashe ba mu sani ba ya tafi ya kashe kansa. Da na bashi da tabin hankali kamar yadda wasu ke tunani sai dai ni ban fahimci abinda ya tunzura shi ya kashe kansa ba."

Kakakin 'yan sandan jihar, SP Gbenga Fadeyi ya ce bankin sun kira su da jami'an kwana-kwana domin a ceto mutumin amma daga bisani aka gano ya riga ya mutu.

Fadeyi ya ce an kai gawar marigayin zuwa asibitin Adeoyo domin binciko dalilin mutuwarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel