Sakamako: PDP lashe zabe a kananan hukumomin Adamawa 14 da aka maimaita zabe

Sakamako: PDP lashe zabe a kananan hukumomin Adamawa 14 da aka maimaita zabe

Jam'iyyar APC mai mulki ta sha kaye a dukkan kananan hukuomin jihar Adamawa 14 da aka maimaita zabe ranar Alhamis, 28 ga watan Maris.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gudanar da zabe a mazabu 44 da ke kananan hukumomi 14 na jihar Adamawa.

A jimillar sakamakon zabe da INEC ta sanar a cibiyoyin tattara sakamako a matakin kananan hukumomi ya nuna cewar Ahmadu Fintiri, dan takarar gwamnan jihar Adamawa a jam'iyyar PDP, na da kuri'u 10,480, yayin da gwamnan jihar, Jibrilla Bindow, mai neman tazarce a karkashin jam'iyyar APC ke da kuri'u 1,391.

Jam'iyyar PDP ta bawa APC tazarar kuri'u 9,089 daga jimillar sakamakon zaben raba gardamar daga kananan hukumomin 14.

Duba sakamakon wasu daga cikin kananan hukumomin;

1. Karamar hukumar Song

Adadin masu kada kuri'a a rijistar zabe – 3833

Adadain masu zabe da aka tantance – 1097

ADC – 4

APC – 406

PDP – 647

Jimillar sahihan kuri'u – 1,060

2. Karamar hukumar Yola ta Kudu

Adadin masu kada kuri'a a rijistar zabe– 4,401

Adadin masu zabe da aka tantance -1,073

ADC – 17

ADA – 9

APC – 188

PDP – 825

Jimillar sahihan kuri'u -1,044

Kuri'un da aka soke – 25

Jimullar kuri'u da aka kada – 1,069

3. Karamar hukumar Girei

Adadin masu zabe a rijista – 1,874

Adadin masu zabe da aka tantance – 563

Adadin kuri'un da aka kada – 557

Sahihan kuri'u – 551

Kuri'un da aka soke – 6

APC – 195

PDP – 352

4. Karamar hukumar Mubi ta Arewa

APC 11

PDP 900

5. Karamar hukumar Michika

APC 187

PDP 1113

6. Karamar hukumar Toungo

PDP 86

APC 2

7. Karamar hukumar Numan

APC 50

PDP 1548

8. Madagali

APC 0

PDP 131

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel