Takaitaccen tarihin Jagoran Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu

Takaitaccen tarihin Jagoran Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu

Yau ne ake bikin cikar Bola Ahmed Tinubu shekara 67 da haihuwa. Mutane da-dama za su so su ji tarihin wannan rikakken ‘Dan siyasa na Yankin Kasar Yarbawa, don haka LEGIT.ng Hausa ta tsakuro kadan daga cikin tarihin sa.

1. Haihuwa da Yarinta

An haifi Asiwaju Bola ahmed Tinini ne a karshen Watan Maris na shekarar 1952 a cikin Garin Legas da ke cikin Kudancin Najeriya. Bayan ya girma ne aka soma kai shi Makarantar Boko a Unguwar Aroloya a Legas.

2. Karatun Boko

Bola Tinubu ya tafi Amurka ne yayi Digiri a wata Jami’a da ke Birnin Chicago a Garin Illinois inda ya karanta harkar Akanta a shekarar 1979. Kafin nan yayi Firamare da Sakandare a cikin Legas da kuma Garin Ibadan.

3. Harkar siyasa

Asiwaju Tinubu ya shiga siyasa ne a karshen mulkin Janar Ibrahim Babangida a 1992. Tinubu yana cikin manyan tafiyar People’s Front da ta narke ta zama jam’iyyar SDP tare da su Janar Shehu Musa Yardua da Rabiu Kwankwaso.

KU KARANTA: INEC ta fito da sabon jadawali na musamman na zaben Jihar Ribas

A lokacin ne ya zama Sanatan Legas ta yamma kafin Janar Sani Abacha ya karbe mulkin kasar a wani juyin. Daga nan ne Tinubu ya kafa kungiyar da ake kira NADECO inda su ka tasa Sani Abacha ya mikawa farar hula mulki.

4. Gwamna a Legas

Bayan an dawo mulkin farar hula ne Asiwaju Tinubu ya nemi takarar Gwamnan jihar Legas a karkashin jam’iyyar AD. An dace Tinubu ya samu tikiti bayan ya sha gumurzu da Wahab Dosunmu da Funsho Williams.

5. Bayan Gwamnan Legas

A 2007 ne Bola Tinubu ya sauka daga gwamna, ya mika mulki ga Babatunde Fashola wanda shi ne shugaban ma’aikatan fadar gidan gwamnati a lokacin sa. Har yau kuma Tinubu yana cikin masu yin ruwa da tsaki a Jihar Legas.

6. Rayuwar yau da gobe

Bola Tinubu yana auren Oluremi Tinubu wanda ta ke wakiltar Legas ta tsakiya a majalisar dattawa. Mahaifiyar Tinubu ta rasu yana da shekaru 62, kuma ya rasa Yaron sa Jide Tinubu a wannan shekarar. Yanzu yana cikin kusoshin APC.

A dalilin Bola Tinubu ne a kan san manya ‘yan siyasa irin su Yemi Osinbajo, Babatunde Fashola, Rauf Aregbesola, Akinwumi Ambode, Lai Mohammed, Tunde Fowler, Remi Tinubu, da kuma Muaz Bunire

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel