Ana wata ga wata: Wata matar aure mai suna Hajara ta mutu a dakin saurayin ta

Ana wata ga wata: Wata matar aure mai suna Hajara ta mutu a dakin saurayin ta

Rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Filato ta kama wani mutum, Gundumi Saya, mai shekaru 42 biyo bayan mutuwar Hajara Markus, wata matar aure da suke soyayya.

Matar auren ta mutu ne a ranar da ta kai wa Saya ziyarar kwana guda.

A cewar rundunar 'yan sanda, Saya; mai mata uku da yara 14, mazaunin Zango-Dinya ne da ke karkashin karamar hukumar Bassa, kuma yanzu haka an gurfanar da shi a gaban kotun jihar Filato da ke Jos a karkashin mai shari'a Daniel Longji.

Ana tuhumar Saya da laifin aikata kisa, wanda ake zargin ya aikata hakan a ranar 21 ga watan Nuwamba na shekarar 2018.

Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewar a ranar 21 ga watan Nuwamba ne, Saya ya aikata laifin zina da matar auren bayan ya yaudare ta domin ya aikata hakan da ita duk da ya san ta na da aure, laifin da rundunar 'yan sanda ta ce ya saba da sashe 368 na kundin aikata laifuka.

Ana wata ga wata: Wata matar aure mai suna Hajara ta mutu a dakin saurayin ta
Wata matar aure mai suna Hajara ta mutu a dakin saurayin ta
Asali: Twitter

Takardar tuhumar mai laifin ta nuna cewar Saya ya faki idon jama'a tare da jefar da gawar Hajara a gefen hanya bayan ya fuskanci cewar ta mutu a lokacin da su ke tare.

Ta kara da cewa wanda ake tuhumar bai yi kokarin sanar da rundunar 'yan sanda ba, wanda hakan laifi ne a karkashin sashe na 189 da na 102 na kundin aikata laifuka.

A jawabin sa, Saya ya musanta cewar ya kashe masoyiyar ta sa, tare da bayyana cewar ya farka ne tsakar dare ya ga ta mutu.

DUBA WANNAN: Karin kudin haraji: Tinubu ya gargadi gwamnatin tarayya

Kazalika ya bayyana cewar sun dade su na soyayya tun kafin mutuwar aurenta na farko da na biyu kafin tayi na uku.

Markus Jagaba, mijin marigayiya Hajara, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewar matar ta sa ta nemi iznin zuwa wurin biki ne a kauyen Jakandangiwa da ke jihar Bauchi.

Za a fara sauraron karar Saya a gaban Jastis Daniel Longji na babbar kotun jihar Filato da ke Jos a ranar 1 ga watan Afrilu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel