Duniya ina zaki damu: A Jigawa wani saurayi ya cire kan dan uwanshi akan saniya

Duniya ina zaki damu: A Jigawa wani saurayi ya cire kan dan uwanshi akan saniya

- Wani saurayi ya saka adda ya guntule kan dan uwanshi a jihar Jigawa

- Hakan ya biyo bayan musun da ya sarke tsakaninsu akan saniya

Hukumar 'yan sanda a jihar Jigawa ta kama wani saurayi dan shekara 22, mai suna Gambo Sa'idu, wanda ke zaune a kauyen Badakoshi, a karamar hukumar Gwaram, da ke jihar Jigawa, da laifin sarewa dan uwanshi kai, yayinda su ke rikici akan wata saniya.

Hassada ta sa wani ya sare kan dan uwanshi a jihar Jigawa
Hassada ta sa wani ya sare kan dan uwanshi a jihar Jigawa
Asali: UGC

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar SP Audu Jinjiri, ya tabbatar da faruwar lamarin, in da ya ce Gambo ya yi amfani da adda ya sare kan dan uwan nashi mai suna Haladu, wanda yake da shekaru 40.

KU KARANTA: Akwai yiwuwar a sake sabon zaben shugaban kasa a Najeriya

Jami'in ya kara da cewa bincike ya nu na cewa wanda ake zargin ya kashe dan uwannashi saboda ya fi shi yawan shanu.

A karshe jami'in ya tabbatar da cewa hukumar zata mika shari'ar wurin hukumar binciken manyan laifuka da ke garin Dutse, babban birnin jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel