Ministan lantarki yace ana kwana a tashi da wuta a wasu wurare a Najeriya

Ministan lantarki yace ana kwana a tashi da wuta a wasu wurare a Najeriya

Mista Babatunde Raji Fashola ya bayyana cewa wasu jihohi a halin yanzu sun daina jin labarin dauke wuta a Najeriya. Ministan harkar wutan lantarki da ayyuka da kuma gidaje ya fadi wannan ne jiya.

Minista Raji Fashola ya fadawa gidan talabijin na Channels TV a jiya Laraba 27 ga Watan Maris cewa an samu karuwar wutan lantarki a fadin kasar nan. Babatunde Fashola yace gwamnatin Buhari ta dage wajen inganta harkar wuta a kasar.

Babban Ministan yake cewa a irin su jihar Kebbi da Yobe da kuma wasu jihohi kusan 10, ana samun wuta dare da rana babu ko kiftawa. Ministan na harkar wuta yace nan gaba zai yi wa jama’a cikakken bayani game da karfin lantarkin.

Raji Fashola yace yanzu abin da Najeriya ta ke samu da kuma jawowa na wutan lantarki ya karu sosai, Ministan yace yanzu haka da ake magana, Najeriya tana samun kusan watt 8, 100 na karfin wuta, wanda ake kuma sa ran zai karu nan gaba.

KU KARANTA: Ana iya sake sabon zaben shugaban kasa a Najeriya

Ministan lantarki yace ana kwana a tashi da wuta a wasu wurare a Najeriya
Ministan wutan lantarki yace ana samun wuta yadda ya kamata
Asali: UGC

Tsohon gwamnan na jihar Legas yace gwamnatin shugaba Buhari ta dauki mataki na narka kudi cikin harkar wuta a Najeriya domin a rage fama da rashin wuta. Wannan ya sa gwamnatin tarayya ta sa kudi har Naira Biliyan 72 wajen sayo kayan aiki.

Bayan nan kuma Ministan gwamnatin tarayyar yace an kawo tsari na raba katin da ke auna wutan da mutum ya sha. Wannan ya taimakawa kamfanonin da aka saidawa wutan lantarkin Najeriya sun samu sa’ida wajen karbar kudi daga hannun jama’a.

Mutanen da ke zaune a irin wadannan wurare watau Yobe da kuma Kebbi kamar yadda Ministan na Najeriya ya fada, sun tabbatar mana da cewa su na samun wutar lantarki sosai a halin yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel