Gobara ta kone gidaje sama da 150 a jihar Jigawa

Gobara ta kone gidaje sama da 150 a jihar Jigawa

- Mutanen wani kauye a jihar Jigawa sun wayi gari cikin wani tashin hankali

- Wata gobara mai karfi ta yi sanadiyyar kone gidaje da dukiya mai tarin yawa a jihar Jigawa

Wani tashin hankali da ya afku a jiya Talata 26 ga watan Maris, a kauyen Barebari dake karamar hukumar Ringim cikin jihar Jigawa. Misalin karfe 11 na safe, mutanen Kauyen wanda yawansu ya kai kimanin 1,000, suka fara jin ihu na neman taimako, ashe wuta ce ta kama kauyen.

Wutar ta yi sanadiyyar konewar gidaje sama da 150. Mutanen kauyen sunyi iya bakin kokarinsu wurin ganin sun kashe wutar amma abin ya ci tura, saboda ba su da isashen ruwa

Gobara ta kone gidaje sama da 150 a jihar Jigawa
Gobara ta kone gidaje sama da 150 a jihar Jigawa
Asali: UGC

An samu saukin kashe wutar ne bayan ma'aikatan kashe gobara sun kawo dauki tare da wasu samari da ke yankin kauyen.

Sai dai kuma babu mutum ko daya da wutar ta kashe, amma wutar ta yi barna da yawa.

Malam Zakari Ya'u daya daga cikin mutanen da gobarar ta shafa yace, wutar ta cinye dukkanin ilahirin gidanshi, ya ce babu wani abu mai amfani da aka iya fitowa dashi daga gidan.

KU KARANTA: An samu gawar wani malamin jami'a a yashe a kasa, bayan kwana hudu ana neman shi

A cewar shi, wutar ta samo asali ne daga wani gidan kara a lokacin da masu gidan suke kokarin dafa abincin karin kumallo, inda a lokacin iska ta dauki wutar ta kama gidan. Ya ce duk da dai ba ayi asarar rai ba amma dabbobi da dama sun kone.

A na shi bayanin, Mai garin na Barebari, Malam Abdu Umar, ya bayyana hakan da kaddara wacce ta riga fata.

Mai garin ya ce mutanen da dama suna kawo musu taimako na kayan abinci, ya zuwa yanzu sun samu sama da buhu 150 na kayan abinci, da kuma kudi kimanin N500,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel