'Yan sanda sunyi zanga-zangar rashin biyansu allawus a Yobe

'Yan sanda sunyi zanga-zangar rashin biyansu allawus a Yobe

Jami'an 'yan sanda na 'Mobile Police' a Jihar Yobe sun bayyana rashin jin dadinsu a kan rashin biyansu allawus din cin abinci har na tsawon watanni hudu.

Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan sandan mobile police dauke da bindigu sun taru a gefen Bankin UBA a kusa da Central Roundabout a ranar Talata inda suka ce za su fara zanga-zanga a kan tituna idan gwamnati ba ta biya su hakokinsu ba.

Daya daga cikin 'yan sandan da bai bayyana sunansa ba saboda tsoron abinda zai biyo baya ya ce rabonsu da samun allawus din cin abinci tun watan Disambar 2018.

DUBA WANNAN: Dattaku: Ganduje ya bayar da umurnin a mayar da hotunan Sarki Sanusi II a gidan gwamnati

'Yan sanda sunyi zanga-zangar rashin biyansu allawus a Yobe
'Yan sanda sunyi zanga-zangar rashin biyansu allawus a Yobe
Asali: Twitter

"Yadda ka ke ganin mu a nan, an turo mu aiki Damaturu ne daga jihohi daban-daban. Tun daga watan Disamban 2018, ba su biya mu allawus din cin abinci ba kuma babu wanda ke yi mana magana a kan lamarin.

"Abin mamaki shine sauran jami'an tsaro kamar sojoji suna samun allawus din su a kan lokaci. Muna son fadar shugaban kasa ta sani cewa ba a biyan mu hakokinmu. Idan ana son rushe atisayen ne, a shirye mu ke mu koma jihohin mu," inji shi.

Wani dan sadan da shima da bai fadi sunansa ba ya ce albashinsa baya isa ya ciyar da kansa da iyalansa.

"A maimakon mu rika amfani da allawus din cin abinci mu rika ciyar da kan mu a nan, muna cin abinci daga albashin mu yayin da yara mu da sauran iyali suna gida ba su iya cin abinci kuma ba mu iya biyan kudin makarantar yaran mu," a cewarsa.

Da aka tuntube shi, Kwamishinan 'yan sanda reshen jihar Yobe, Abdulmaliki Sunmonu ya ce bashi da masaniya cewa akwai dan sandan mobile din da ba a biya shi allawus ba.

"Idan ma akwai wadanda ba a biya ba, ba su sanar da mu ba. Ina son in san ko su wanene wadandan mutanen. Watakila suna da matsala da bankunansu ne amma babu jami'in da ke bin mu bashi," inji Sunmonu.

Da aka tambaye shi ko akwai wadanda ba a biya allawus din cin abinci ba ya ce, "A'a, mun biya kowa. Na gode".

DUBA WANNAN: Dattaku: Ganduje ya bayar da umurnin a mayar da hotunan Sarki Sanusi II a gidan gwamnati

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel