Ahmad Sulaiman zai dawo gida bayan ya shafe kwanaki 13 a tsare

Ahmad Sulaiman zai dawo gida bayan ya shafe kwanaki 13 a tsare

- An saki Alaranman Izalan nan Ahmad Sulaiman Ibrahim

- Yanzu haka yana kan hanyar komawa gidan sa da ke Kano

- Malamin ya shafe kusan makonni 2 tsare a hannun Miyagu

Babban Malamin nan na cikin Garin Kano watau Ahmad Sulaiman zai samu dawowa gidansa bayan wasu masu garkuwa da mutane sun sace sa kwanaki. A Yau dinann 27 ga Watan Maris mu ka samu wannan labari na farin ciki.

Jaridar Daily Trust ta tabbatar mana da cewa Shehin ya kusa dawo gida yanzu haka. Malam Muhammad Kabir, shi ne wanda ya bayyana wannan a madadin Iyalin wannan Bawan Allah da aka sace tun kusan makonni 2 da su ka wuce.

KU KARANTA: Alaramma Ahmad Sulaiman ya roki jama'a su kawo masa agaji

Ahmad Sulaiman zai dawo gida bayan ya shafe kwanaki 13 a tsare
Ahmad Sulaiman ya fito bayan jama'a sun yi ta faman addu'o'i
Asali: UGC

Muhammad Kabir yake cewa yanzu Sheikh Ahmad Sulaiman yana kan hanyar dawowa gidan sa da ke Kano bayan ya samu ya kubuta daga hannun wadanda su ka tsare sa. An sace Malamin ne a hanyar sa ta zuwa Birinin Kebbi.

Masu garkuwa da mutanen sun dura kan Ahmad Sulaiman Ibrahim da kuma wasu malaman addinin musulunci 5 a daidai a hanyar Sheme zuwa cikin Kankara kafin su karasa zuwa wajen wani wa’azi da za ayi a cikin jihar Kebbi.

Kwanaki kun ji cewa masu garkuwa da mutanen da su ka sace Malamin su na ta faman tattaunawa da Iyalinsa domin ganin an biya kudi kafin su sake sa. Yanzu dai ba mu da labarin ko an bada wasu kudin fansa kafin ya bar hannun su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel