Zargin ta'annati da dukiya yayin yakin zabe - Buhari da Atiku za su gurfana a ranar 7 ga watan Mayu

Zargin ta'annati da dukiya yayin yakin zabe - Buhari da Atiku za su gurfana a ranar 7 ga watan Mayu

Babbar Kotun tarayya da ke zaman ta a garin Abuja, ta kayyade ranar 7 ga watan Mayu a matsayin ranar da za ta ci gaba da sauraron korafi na neman tabbatar da rashin cancantar takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Atiku Abubakar a babban zabe na bana.

A ranar Talata 7 ga watan Mayu, babbar kotun tarayya za ta ci gaba da sauraron korafi na neman haramta cancantar takarar shugaban kasa Buhari da kuma Atiku ta zaben kujerar shugaban kasa a sakamakon sabawa doka wajen ta'annati da dukiya yayin yakin neman zaben su.

Zargin ta'annati da dukiya yayin yakin zabe - Buhari da Atiku za su gurfana a ranar 7 ga watan Mayu
Zargin ta'annati da dukiya yayin yakin zabe - Buhari da Atiku za su gurfana a ranar 7 ga watan Mayu
Asali: UGC

Usman Ibrahim Alhaji, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar NRM, National Rescue Movement, shi ne ya maka jiga-jigan 'yan takarar biyu a gaban Kuliya sakamakon yadda kowanen su ya batar da fiye da naira biliyan daya wajen gudanar da yakin neman zabe.

Ibrahim Alhaji ya nemi kotun ta ribaci hukuncin sashe na 91 sakin layi na biyu cikin dokokin hukumar zabe domin haramta cancantar takarar Atiku da Buhari yayin zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.

KARANTA KUMA: Kasafin Kudi: Ban ji dadin yadda Majalisar Saraki ta mu'amalanci gwamnati na ba - Buhari

Mai shigar da korafin da sanadin Lauya sa, Mista Ezkiel Ofou, ya yi korafin cewa a yayin da Buhari da Atiku suka sabawa doka na kashe fiye da Naira biliyan daya wajen gudanar da yakin su na neman zabe, hukunci na haramcin takara zai wajaba a kansu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel