Gwamna Abubakar bai amince ya sha kashi a zaben Bauchi ba tukun

Gwamna Abubakar bai amince ya sha kashi a zaben Bauchi ba tukun

Mai Gwamnan Jihar Bauchi, Muhammad Abubakar ya musanya rahotannin da ke yawo na cewa ya fito ya taya ‘dan takarar jam’iyyar PDP a zaben jihar watau Bala Mohammed murnar samun nasara.

Gwamnan na Bauchi yayi wannan jawabi ne ta bakin babban Sakataren sa na yada labarai, Abubakar Alsadique. Dazu aka rika jin labari na yawo cewa Gwamna Muhammad Abubakar ya saduda ya amince da shan kayi a zaben.

Gwamnan yake cewa hankalin su ya zo kan wata jita-jita da ake yi na cewa har yayi maza ya taya Abokin hamayyar sa murna na lashe zaben da aka yi. Babban mai magana da yawun bakin gwamnan yace babu gaskiya a labarin.

KU KARANTA: INEC ta maye gurbin ‘Dan Majalisar da ya rasu ana shirin zabe

Gwamna Abubakar bai amince ya sha kashi a zaben Bauchi ba tukun
Gwamna M.A yace bai taya Kauran Bauchi murnar nasara ba
Asali: Twitter

Muhammad Abubakar ya musanya wannan rahoto da ya bi gari inda yace labari ne kurum irin na rediyo mai jini don haka yayi kira ga jama’a su yi watsi da wannan labari. Abubakar Alsadique yace sam bai fitar da wannan jawabi ba.

Mai magana da yawun bakin Gwamnan yace su na da hanyoyin ganawa da manema labarai idan har za a fitar da wani jawabi, inda yace a wannan karo gwamna bai zanta da ‘yan jarida, har yayi jawabin taya PDP murnar cin zabe ba.

Yanzu an koma cigaba da tattara sakamakon zaben da aka yi a cikin karamar hukumar Tafawa-Balewa da ta rage. A zaben cike-gibi da aka yi a Ranar Asabar, jam’iyyar PDP ce ta lallasa APC mai mulki a jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel