PDP ta buga magudi na Inna-naha a zaben Tambuwal inji APC

PDP ta buga magudi na Inna-naha a zaben Tambuwal inji APC

- APC tace zaben da Tambuwal ya ci ya zo da wasu haka-da-haka

- Jam'iyyar tace PDP ta buga magudi wajen samun nasara a zaben

- Hakan na zuwa ne bayan 'Dan takarar APC ya taya PDP murna jiya

Jam’iyyar APC ta reshen jihar Sokoto ta bayyana cewa bata amince da sakamakon zaben gwamna da aka kammala a cikin karshen makon nan da ya gabata ba. A jiya Lahadi 24 ga Watan Maris ne INEC ta sanar cewa PDP ta ci zaben Sokoto.

APC ta bangaren Sokoto ta yi watsi da wannan zabe da aka yi inda tace an tafka ba daidai ba a zaben. Jam’iyyar mai mulkin kasar ta yi wannan jawabi ne ta bakin Kakakin ta na jihar Sokoto watau Alhaji Bello Danchadi a jiya da yamma.

KU KARANTA: Tsohon Shugaba Obasanjo ya fadawa Atiku ya sheka Kotu

PDP ta buga magudi na Inna-naha a zaben Tambuwal inji APC
Jam'iyyar APC tace an yi magudi a zaben Jihar Sokoto
Asali: Facebook

Bello Danchadi yake cewa ratar da ke tsakanin jam’iyyar PDP da kuma APC na kuri’a 342 ba su isa ace sun ba mutum nasara a jihar Sokoto ba. Danchadi yake cewa akwai sama da mutane 342 da su kayi rajista a wuraren da aka soke zaben jihar.

Wannan ya sa Mai magana da yawun jam’iyyar yake ganin sanar da Gwamna mai-ci Aminu Tamuwal a matsayin wanda ya lashe zaben jihar ya sabawa dokar hukumar zabe na kasa mai zaman kan-ta. APC ta kuma ce PDP ta zuba magudi a zaben.

Jam’iyyar ta APC tace ta kai kukan ta gaban hukumar INEC game da irin magudin da aka tafka a Sokoto ta hanyar hana wasu kada kuri’ar su, yayin da a wasu wurare aka rika amfani da ‘yan daba wajen yin murdiya don haka APC tayi tir da zaben.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng