Yadda PDP ta ci zaben gwamnan Sokoto da tazara ma fi karanci a tarihi
Aminu Waziri Tambuwal, dan takarar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, ya samu nasarar yin tazarce a kan kujerar sa ta gwamnan jihar Sokoto da tazarar kuri’u ma fi kankanta bayan kamala tattara sakamako daga kananan hukumomi 22 da aka maimaita zabe a jiya, Asabar.
An tattara tare da sanar da sakamakon zaben gardama a hedikwatar hukumar zabe ta kasa (INEC) dake garin Sokoto.
A zaben ranar Asabar, 9 ga watan Maris da INEC ta bayyana cewar bai kammmalu ba, jam’iyyar PDP na da kuri’u 489,558, yayin da jam’iyyar APC da Ahmad Aliyu ke yiwa takara ta samu kuri’u 486,145.
A wancan lokacin, jam’iyyar PDP a kan gaba da tazarar kuri’u 3,413 amma saboda soke wasu kuri’u a a akwatinan zabe 136 dake kananan hukumomi 22 da adadin masu rijistar zabe 75,403, INEC ta ce sai an je zagaye na biyu domin kece raini kamar yadda doka ta tanada.
A yayin da ya rage saura sakamakon zabe daga karamar hukumar Kebbe a sanar da sakamakon zaben gwamna a jihar Sokoto, jam'iyyar PDP na da jimillar kuri'u Jimilla kuri'u 18342 daga mazabun da aka maimaita zabe, yayin da APC ke da adadin kuri'u 16987.
A sakamakon zaben karamar hukumar Kebbe da aka sanar, jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 5,457, yayin da APC ta samu kuri’u 7,173.
DUBA WANNAN: Kotu ta bayyana yadda INEC ta canja sakamakon zaben gwamna a Osun
A sakamakon zabe na karshe da baturiyar zabe, Farfesa Fatima Batulu Mukhtar, ta sanar, jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 25,857, yayin da APC ta samu kuri’u 25,515. Bayan an kara sakamakon zaben raba gardamar a kan tsohon sakamakon zaben dake hannun INEC, Aminu Waziri Tambuwal na jam’iyyar PDP ya samu jimillar kuri’u 512,002, yayin da Ahmad Aliyu na jam’iyyar APC ya samu jimillar kuri’u 511,661.
A saboda haka, jam’iyyar PDP ta kayar da APC da tazarar kuri’u 341. Tazarar da masu bibiyar lamuran siyasa da zabe a Najeriya ke ganin ba a taba samun mai kankantar ba a zaben kujerar gwamna.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng