Atiku ne ya ci zaben shugaban kasa a Kaduna a mafarkin sa – El-Rufa’i

Atiku ne ya ci zaben shugaban kasa a Kaduna a mafarkin sa – El-Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya yiwa dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP shagube ta hanyar bayyana cewar shine ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Kaduna.

Da farko na dauka wasa ne amma da duba sosai sai naga da gaske ne ya furta cewar ya lashe zabe a jihar Kaduna. Ina ganin a mafarkin shi ne hakan ta faru,” a cewar El-Rufa’i yayin gana wa da manema labarai a fadar shugaban kasa a ranar Juma’a.

Sannan ya kara da cewa, “Ko za a sake zabe sau 10 ba zai yi nasara a jihar Kaduna ba don bait aba ci zabe a jihar ba.”

Atiku na kalubalantar nasarar da shugaba Buhari ya samu a zaben shugaban kasa da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta gudanar ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, ya bayyana cewar bayanan daga daga na'urar hukumar zabe ta kasa (INEC) sun nuna yadda aka rage ma sa kuri'u a zaben shugaban kasa a jihohi 31 da birnin tarayya, Abuja.

Atiku ne ya ci zaben shugaban kasa a Kaduna a mafarkin sa – El-Rufa’i
El-Rufa’i
Asali: UGC

Atiku ya bayyana hakan ne a cikin takardar karar da ya shigar gaban koton sauraron korafe-korafe a kan zaben shugaban kasa. Dan takara na PDP ya bayyana cewar ya kayar da shugaba Buhari da tazarar kuri'u 1,615,302.

Ya ce na'urar hukumar INEC ta nuna cewar ya samu adadin kuri'u 18,356,732 da suka bashi rinjaye a kan shugaba Buhari, wanda ya samu kuri'u 16,741,430. A ranar 27 ga watan Fabrairu ne hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana shugaba Buhari na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar shugaban kasa.

DUBA WANNAN: An sake kai hari kan wasu Masallatai 5 a Ingila

A sanarwar INEC ta bakin shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shugaba Buhari na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 15,191,847 yayin da babban abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 11,262,978.

Atiku ya ce na'urar tantance masu zabe na aika sakamakon zabe daga kowacce akwati zuwa babbar na'urar hukumar INEC. Ya kara da cewa INEC ta fitar da adadin mutanen da ta yiwa rijista kafin zabe amma kuma ta shigar da wani adadi na daban a fom din EC8D(A).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel