Gobara ta lalata kayan dalibai fiye da 190 a Jigawa

Gobara ta lalata kayan dalibai fiye da 190 a Jigawa

Gobarar ta da faru a cikin kwana-kwanan nan a makarantun sakandire biyu a jihar Jigawa ta lalata kayayakin dalibai guda 196 kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Makarantun da gobarar ta shafa sun hada da Makarantar Sakandire na Kimiyya, Lautai, Gumel da Commercial Secondary School da ke Takur Addua a Dutse.

Gobarar ta makarantar sakandire na Lautai da ke karamar hukuma Gumel ta tashi ne a dakin kwanan dalibai inda ta lalata musu kayansu da suka hada da takardun karatu, tufafi, katifun kwanciya da kayan abinci.

DUBA WANNAN: 'Yan kungiyar Boko haram sun shiga matsala: Wani hakimi ya tona musu asiri

Gobara ta lalata kayan dalibai fiye da 190 a Jigawa
Gobara ta lalata kayan dalibai fiye da 190 a Jigawa
Asali: UGC

Sakataren Hukumar Kula da Makarantun Kimiyya da Fasaha na jihar, Mallam Haladu Yakubu ya ce gobarar ta faru ne a ranar Talata yayin da daliban ke aji suna karbar darrusa.

Wata gobarar kuma da ta faru a dakin dalibai na Commercial Secondary School, Takur Adua tayi sanadiyar asarar kayan dalibai 100.

Mallam Abdullahi Yunusua, shugaban Hukumar Kula da Harkokin Ilimi na jihar (SEIMU) ya ce gobarar tayi illa sosai a dakunan dalibai guda uku inda ya kara da cewa gwamnatin jihar ta aike da tawaga na musamman domin gudanar da bincike a kan afkuwar lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164