CP Mohammed Wakili 'Singham' ya nemi afuwar kungiyar NBA reshen Kano
Rundunar 'yan sanda reshen Jihar Kano ya nemi afuwar Kungiyar Lauyoyi na Kasa, NBA, reshen Jihar Kano a kan zargin cin zarafi da hari da aka kaiwa wasu lauyoyi a jihar.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Mr Wakili Muhammad ne ya nemi afuwar a yayin da ya kai ziyara hedkwatan NBA da ke Farm Centre a cikin birnin Kano.
Muhammad ya ce lauyoyi abokan tafiya ne hakan yasa ya dauki matakin neman afuwar kungiyar domin neman yafiyarsu da cigaba da aiki tare.
DUBA WANNAN: 'Yan kungiyar Boko haram sun shiga matsala: Wani hakimi ya tona musu asiri

Asali: Twitter
"Aiki na ba zai yiwu ba sai da lauyoyi, ina fatan za mu cigaba da aiki tare bisa yadda doka ta tanadar," inji shi.
Muhammad ya ce a shirye ya ke ya nemi afuwar kungiyar ta kowane hali da suke bukata; Ta hanyar rubuta wasika ko kuma ta kafar watsa labarai.
A bangarensa, shugaban kungiyar na jihar Kano, Musa Abdullahi Lawal ya mika godiyarsa ga Kwamishinan 'yan sandan bisa ziyarar da ya kai musu.
Ya ce kungiyar a shirye ta ke tayi aiki tare da 'yan sanda domin ganin an tabbatar da adalci.
A jiya (Laraba) ne NBA ta bawa rundunar 'yan sandan wa'addin sa'o'i 48 domin ta nemi afuwar kungiyar a kan cikin zarafin mambobinta da akayi yayin da suke gudanar da ayyukansu kamar yadda NAN ta ruwaito.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng