Rai bakon duniya: El-Rufai ya kai ma Alu Wammako ziyarar ta’aziyya

Rai bakon duniya: El-Rufai ya kai ma Alu Wammako ziyarar ta’aziyya

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya kai ziyarar ta’aziyya zuwa gidan tsohon gwamnan jahar Sakkwato, kuma shugaban Sanatocin Arewacin Najeriya, Sanata Aliyu Magatakardan Wammako bisa rasuwar kaninsa.

El-Rufai ya bayyana haka ne a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook a ranar Alhamis 21 ga watan Maris, inda yace ya kai ziyarar ne don jajanta ma Wammako sakamakon rasuwar kaninsa, Salihu Baraden Wammako.

KU KARANTA: NNPC ta bayyana adadin biliyoyin litan mai data tura sassan kasar nan

Rai bakon duniya: El-Rufai ya kai ma Alu Wammako ziyarar ta’aziyya
El-Rufai da Alu
Asali: Facebook

“A yau na kai ziyarar ta’aziyya tare da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jahar Kaduna, Alhaji Bashir Saidu zuwa gidan Sanata Aliyu Wammako don jajanta masa bisa rasuwar kaninsa, Alhaji Salihu Baraden Wammako.” Inji El-Rufai.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Kaduna ya dawo gida Najeriya bayan wani dan gajeren tafiya da yayi, inda tafiyan nasa keda wuya magauta suka fara watsa jita jitan cewa wai ya gamu da mummunan hatsari akan hanya, kuma direbansa ma ya mutu.

Rai bakon duniya: El-Rufai ya kai ma Alu Wammako ziyarar ta’aziyya
Rai bakon duniya: El-Rufai ya kai ma Alu Wammako ziyarar ta’aziyya
Asali: Facebook

Legit.ng ta ruwaito kaakakin gwamnan, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da dawowar maigidan nasa, inda yace El-Rufai ya iso filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikwe ne tsakar ranar Laraba, 20 ga watan Maris.

Shima gwamnan ya karyata batun a shafinsa na Facebook, inda yace “Na farka daga dogon barci na tsawon sa’o’I 8 wanda ban ma saba ba, kawai sai naji jita jitan wa ina cikin mawuyacin hali, kuma direbana ya mutu, amma na san aikin PDP ne wannan, kuma duk karyace.

“Nagode da suke rage kwanakinsu a duniya suna karamin, kuma zan cigaba da kasancewa dodonsu, kuma b azan gushe daga rayuwarsu ta sata da rashawa anan kusa ba da ikon Allah, har sai na yi musu ritaya, kuma na kashesu.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel