Zaben cike gurbi a jihar Bauchi da Adamawa na nan daram kamar yadda muka tanada - INEC

Zaben cike gurbi a jihar Bauchi da Adamawa na nan daram kamar yadda muka tanada - INEC

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC, ta yi watsi da umurnin Kotu da cewa zaben cike gurbi zai gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Maris cikin jihohin Adamawa da kuma Bauchi kamar yadda ta shar'anta.

INEC ta ce takaddamar shigar korafi kan zaben cike-gurbi a jihar Bauchi ta samo tushe da kuma asali daga bangaren jam'iyyar APC da kuma dan takarar ta kujerar gwamnan jihar, Muhammadu Abubakar.

Zaben cike gurbi a jihar Bauchi da Adamawa na nan daram kamar yadda muka tanada - INEC
Zaben cike gurbi a jihar Bauchi da Adamawa na nan daram kamar yadda muka tanada - INEC
Asali: UGC

Cikin sanarwar da wallafa a shafin ta na sada zumuntar Twitter a ranar Alhamis, 21 ga watan Maris, INEC ta ce bisa ga tanadin doka da kuma shimfidar tsare-tsaren kundin tsarin mulkin kasa, kotu ba ta da hurumin sanya ma ta takunkumi yayin sauke nauyin da rataya a wuyanta.

Sai dai ta ce hukuncin kotun zai shafi dakatar da ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamna na karamar hukumar Tafawa Balewa da ke jihar. Ta ce zaben cike-gurbin zai gudana a ranar Asabar 23, ga watan Maris kamar yadda ta shar'anta cikin kakanan 15 na jihar.

KARANTA KUMA: Garkuwa da Mutane, Satar Shanu, rikicin Makiyaya da Manoma sun fi ta'addancin Boko Haram muni - Dan Ali

Kazalika INEC ta ce ta yi watsi da hukuncin babbar Kotu inda za ta gudanar da zaben cike gurbi na gwamnan jihar Adamawa cikin kananan hukumomin Nassarawo, Mayo, Belwa, Uba da kuma Gaya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel