Abin da ya sa aka maida Kotun korafin zaben Taraba zuwa Garin Abuja

Abin da ya sa aka maida Kotun korafin zaben Taraba zuwa Garin Abuja

Jaridar nan ta Leadership ta rahoto cewa Kotun da zai saurari korafe-korafe game da zaben gwamna da aka yi a jihar Taraba, ta tashi daga cikin jihar inda ta koma zuwa babban birnin tarayya da ke Abuja.

An maida zaman shari’ar zuwa Abuja ne a bisa la’akari da hali na tsaro da ake ciki a Garin Jalingon jihar Taraba. Sakataren wannan kotu na musamman da shugaban kotun daukaka kara watau Z A. Bukachuwa ta kafa ya bayyana wannan.

KU KARANTA: Kotu za ta yanke hukunci game da zaben Gwamnan Osun gobe

Abin da ya sa aka maida Kotun korafin zaben Taraba zuwa Garin Abuja
‘Yan takara 7 sun kai karar zaben Taraba gaban Kotu
Asali: UGC

Alkali Julde Abdulsalam wanda shi ne Sakataren wannan Kwamiti na Alkalai da za su saurari karar zaben Taraba yake cewa dauke shari’ar daga Jalingo zuwa Abuja ya fi zama lafiya ga Lauyoyi da sauran wadanda za a bukaci gani a gaban kuliya.

Julde Abdulsalam ya fadawa manema labarai cewa harka ta tsaro ce ya sa su ka dauke shari’ar zuwa babban birnin tarayya inda ya kuma cewa kawo yanzu sun samu korafi akalla 7 a game da manyan zabukan da aka yi a jihar cikin kwanakin nan.

Sakataren kotun karbar karan zaben yace akwai korafi game da zaben Sanatoci 3 da aka yin a jihar, sannan kuma wasu ‘yan takarar majalisar tarayya 4 su na kalubalantar zaben da aka yi a jihar. Sai dai har yanzu ba a tuhumar zaben gwamna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel