Gwamnatin Ganduje tana farautar wani dan jarida ruwa a jallo

Gwamnatin Ganduje tana farautar wani dan jarida ruwa a jallo

Wani shahararren dan jarida a jahar Kano, Yakubu Musa Fegge ya aika ma kwamishinan Yansandan jahar Kano, Muhammad Wakili Singham takardar koke game da barazana da yace gwamnatin jahar Kano na yi ma rayuwarsa.

Takardar dake dauke da sa hannun lauyan Yakubu Musa, Abba Hikima ta bayyana cewa wasu hadiman gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje suna yi ma rayuwarsa barazana, tare da wasu matasa da suka dauki alwashin yin maganinsu sakamakon suna yi ma tazarcen Ganduje barazana.

KU KARANTA: Buhari zai kaddamar da kasuwar bajekoli ta Duniya a jahar Kaduna

A cewar Fagge, da misalin karfe 7 na daren Talata, 19 ga watan Maris aka kirashi ta waya da wata bakuwar lamba, inda aka ja kunnensa game da hukuncin da wasu hadiman gwamna suka yanke akansa matukar bai daina abinda suka kira a matsayin zagon kasa ga gwamnatin Ganduje ba.

“Da wannan da kuma ganin cewa tsarin shari’ar kotu ta fi zama masalha ga daukan doka a hannu, tasa muka muka sanar da kai abinda ke faruwa domin ka gudanar da bincike, muna da tabbacin rayuwar wanda muke karewa tana cikin hadari.” Inji lauyan.

A wani labarin kuma, Al’ummar mazabar Gama sun yi fitar farin dango don tarbar gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yayin daya kai ziyarar aiki zuwa mazabar da nufin gane ma idanunsa matsayin aikin sabon titin da aka fara a makon data gabata.

Legit.ng ta ruwaito a ranar Litinin, 18 ga watan Maris ne Gwamna Ganduje ya kai wannan ziyarar aiki, amma isarsa keda wuya sai ga daruruwan mutane sun mamayeshi, suna yi masa fatan alheri, tare da addu’ar samun nasararsa a zaben gwamnan jahar dake karatowa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel