Ministan kimiyya ya sa APC ta sha kasa a Ebonyi – Inji Kungiyar DV

Ministan kimiyya ya sa APC ta sha kasa a Ebonyi – Inji Kungiyar DV

Kungiyar nan ta Democratic Vanguard (DV) na Jam’iyyar APC ta daura laifin shan kasa da jam’iyyar tayi a jihar Ebonyi a zaben gwamnoni da ‘yan majalisa a kan Minista Dr Ogbonnaya Onu.

Kamar yadda wasu jaridun kasar nan su ka rahoto, shugaban kungiyar Democratic Vanguard na ‘Ya ‘yan APC a Jihar Ebonyi watau Vincent Uzor, yace Ministan kimiyya Ogbonnaya Onu ya jawo masu rashin nasara a zaben gwamna.

A jawabin da Vincent Uzor yayi Ranar Laraba 20 ga Watan Maris a cikin Garin Abakiliki, ya bayyana cewa babban Ministan kasar ya zare hannun sa ne daga duk wani abu da ya shafi yakin neman zaben jam’iyyar APC a jihar Ebonyi.

Mista Uzor yake cewa Ministan kimiyya da fasahan Najeriya ne yayi wa jam’iyyar APC zagon kasa a gida. Shugaban wannan kungiya yake cewa Dr Ogbonnaya Onu ne ya kawowa APC cikas wajen karbe mulki daga hannun PDP a jihar.

KU KARANTA: Babu makaki INEC tayi watsi da zaben cike gibi a Jihar Adamawa

Ministan kimiyya ya sa APC ta sha kasa a Ebonyi – Inji Kungiyar DV
An zargi Ministan kimiyya da yi wa APC zagon-kasa a zaben 2019
Asali: UGC

‘Ya ‘yan wannan kungiya da ke cikin APC sun bayyana cewa tun kafin a kai ko ina, har Ministan ya fara harin kujerar shugaban kasa. Uzor yace Ogbonnoya Onu ya kudiri wannan shiri ne kafin a rantsar da shugaban kasa Buhari a karo na biyu.

Vincent Uzor yace ko kadan Ministan na Buhari bai yi wa APC aikin da ya dace na hada-kan ‘yan takarar APC a jihar da kuma kawo jami’an tsaro da bada gudumuwar kudi wajen ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaben da aka yi kwanan nan ba.

Duk da APC ta sha kashi, kungiyar tace a maimakon Onu ya zauna ya ga inda aka samu kuskure, amma sai ya fara shirin kaddamar da wadanda za su yi masa yakin neman zaben shugaban kasa a zaben 2023. Tuni dai Ministan ya karyar zargin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel