Babu tabbacin gudanar da zaben kece raini a jihar Adamawa - INEC
Ba lallai zaben zagaye na biyu na kece raini da hukumar zabe ta kasa (INEC) ke shirin gudanarwa a jihar Aadamawa ya yiwu saboda hukuncin da ake saka ran kotu zata yanke a gobe, Alhamis.
Kwamishinan hukumar INEC a jihar Adamawa, Barista Kassim Gaidam, ya shaidawa manema labarai yau, Laraba, a Abuja cewar duk da INEC ta kammala dukkan shirye-shirye domin gudanar da zaben, hukuncin da kotun zata yi gobe shine zai tabbatar ko zaben zai yiwu ko akasin haka.
A baya kwamishinan ya bayyana cewar kotu ba ta da ikon dakatar da INEC daga gudanar da zaben kece rainin, ya na mai kafa hujja da wasu dokokin zabe.
A ranar Juma'a, 14 ga watan Maris ne, Jastis Abdul-Azeez Waziri na babbar kotun jihar Adamawa da ke Yola ya umarci INEC ta dakatar da gudanar da zaben har sai an saurari wani korafi da aka shigar kotun.

Source: UGC
Dan takarar gwamna a jam'iyyar MRDD, Eric Theman, ne ya shigar da korafi a gaban kotun bisa zargin cewar babu alamar jam'iyyar sa a jikin kuri'a.
"A matsayin mu na hukuma mai mutunta doka, zamu yi biyayya ga umarnin kotu a kan zaben da za a maimaita," a cewar kwamishinan cikin wani salo da za a iya fassara shi da mi'ara koma baya.
DUBA WANNAN: Maimaita zabe: Rundunar sojin sama ta fara jigilar kayan aiki zuwa jihohi
Ya kara da cewa INEC ta tura tawagar manyan lauyoyi daga hedikwatar ta dake Abuja domin su kare ta a karar da za a saurara a gobe.
Jam'iyyar APC da PDP na da damar samun nasara 50/50 a jihar Adamawa matukar kotu ta umarci INEC ta saka alamar jam'iyyar MRDD a jikin kuri'a kuma ta saka sabon zabe.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng