Yadda cutar Kanjamau ta yi tasiri cikin jihohin Najeriya
Cibiyar gudanar da bincike akan tasiri da yaduwar cutar Kanjamau ta Najeriya, ta fitar da wata sabuwar kididdiga dangane da yadda cutar Kanjamau mai karya garkuwar jiki ta yi tasiri cikin dukkanin jihohi 36 da ke fadin kasar nan.
Kamar yadda kididdigar ta bayyana, akwai adadin al'ummar Najeriya miliyan 1.9 masu dauke da cutar Kanjamau inda jihar Akwa Ibom ta ke a mataki na farko, yayin da jihar Benuwe da kuma Ribas suka biyo baya.
KARANTA KUMA: Zaben Najeriya abun kunya ne a idon duniya - Amurka
Shafin jaridar Premium Times ya ruwaito cewa, kimanin kaso 1 cikin 100 na adadin al'ummar Najeriya na rayuwa dauke da cutar Kanjamau.
Filla-Filla ga yadda kaso na adadin al'umma masu dauke da cutar kanjamau ya ke cikin jihohin Najeriya a mahanga ta kasancewar ta ruwan dare.
Akwa Ibom - 5.5%
Benue - 5.3%
Rivers - 3.8%
Taraba - 2.9%
Anambra - 2.4%
Abia - 2.1%
Cross River - 2.0%
Enugu - 2.0%
Nassarawa - 2.0%
Bayelsa - 1.9%
Delta - 1.9%
Edo - 1.9%
Imo - 1.8%
Ogun - 1.6%
Plateau - 1.6%
Abuja - 1.6%
Lagos - 1.4%
Gombe - 1.3%
Adamawa - 1.2%
Borno - 1.2%
Kaduna - 1.1%
Ondo - 1.1%
Kwara - 1.0%
Kogi - 0.9%
Osun - 0.9%
Oyo - 0.9%
Ebonyi - 0.8%
Ekiti - 0.8%
Niger - 0.7%
Kano - 0.6%
Kebbi - 0.6%
Bauchi - 0.5%
Zamfara - 0.5%
Sokoto - 0.4%
Yobe - 0.4%
Jigawa - 0.3%
Katsina - 0.3%
Ga yadda tasirin cutar yake a yankuna 6 da Najeriya ta kunsa
Kudu maso Kudu - 3.1%
Arewa ta Tsakiya - 2.1%
Kudu maso Gabas - 1.9%
Kudu maso Yamma - 1.2%
Arewa maso Gabas - 1.1%
Arewa maso Yamma - 0.6%
A ranar Alhamis 14 ga watan Maris, cibiyar kula da yaduwar cutar kanjamau ta NACA, National Agency for Control of Aids, ta bayyana cewa yankin Kudu maso Kudu na Najeriya na tattare da mafi girman kaso na adadin al'umma masu da dauke da cutar Kanjamau.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng