Zaben Gwamnan Kano: Kwamishina ‘Maza kwaya Mata kwaya’ ya kai ma Malaman Darika ziyara

Zaben Gwamnan Kano: Kwamishina ‘Maza kwaya Mata kwaya’ ya kai ma Malaman Darika ziyara

Shahararren kwamishinan Yansandan jahar Kano, Muhammad Wakili, wanda aka fi sani da suna Singham, ko kuma ‘Maza kwaya Mata kwaya, ya kai ma shuwagabannin kungiyar Malaman darikar Tijjaniyyah ziyara na jahar Kano.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kwamishina Singham ya kai ma Malaman wannan ziyara ne a ranar Asabar, 16 ga watan Maris na shekarar 2019, inda ya samu shuwagabannin darikan a babban ofishin kungiyar samarin Tijjaniyya dake Kano.

KU KARANTA: Dubu ta cika: Yadda wasu gagararrun yan fashi da makami suka fada komar Yansanda

Zaben Gwamnan Kano: Kwamishina ‘Maza kwaya Mata kwaya’ ya kai ma Malaman Darika ziyara
Wakili
Asali: Facebook

A yayin ziyarar tasa, Singham ya bayyana godiyarsa ga Malaman bisa kyawawan addu’o’in da suke yi na samun zaman lafiya dawwamamme a jahar Kano, da ma kasa Najeriya gaba daya.

Idan za’a tuna, a ranar Asabar din ne kwamishina Muhammad Wakili ya kai ziyara ga shugaban kungiyar izalatil bidi’a wa iqamatissunnah reshen jahar Kano, Malam Abdullahi Saleh Pakistan a ofishinsa.

Kwamishinan ya bayyana makasudin ziyarar daya kai ma Malamin, inda yace yayi haka ne don nuna girmamawa, tare da bayyana godiya ga yadda kungiyar take basu gudunmuwa game da aikin da rundunar take yi a jahar Kano.

Zaben Gwamnan Kano: Kwamishina ‘Maza kwaya Mata kwaya’ ya kai ma Malaman Darika ziyara
Wakili
Asali: Facebook

Shima a jawabinsa, Malam Pakistan ya yi kira ga kwamishinan daya ji tsoron Allah a duk aikin dayake yi, domin kuwa Allah zai tambayeshi game da duk abinda yayi, don haka ya gargadeshi daya ji tsoron Allah.

Daga karshe shima Wakili ya bayyana godiyarsa ga Malam Pakistan, musamman game da nasihar da yayi masa, don haka yace shi ba zai yarda ya sayar da lahirarsa saboda duniya ba, ba zai yarda ya kasance dan asara ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng