SPIP: Kwamitin Shugaba Buhari yana bijerewa Mataimakin Shugaban kasa

SPIP: Kwamitin Shugaba Buhari yana bijerewa Mataimakin Shugaban kasa

Fiye da shekara guda kenan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada kwamitin da zai rika bincike a game da kadarori da dukiyar al’umma da gwamnati ta karbe daga wasu ‘yan siyasa.

SPIP: Kwamitin Shugaba Buhari yana bijerewa Mataimakin Shugaban kasa
Okoi Obla yana yi wa Mataimakin Shugaban kasa abin da ya ga dama
Asali: Facebook

Sai dai daga kafa wannan kwamiti zuwa yanzu, an same sa da bijerewa Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo. Jaridar Premium Times tace wannan kwamiti yana sabawa umarnin fadar shugaban kasa a aikin da yake yi.

Jaridar tace Farfesa Yemi Osinbajo yayi ta kokarin fadawa shugaban wannan kwamiti na SPIP, Okoi Obono-Obla, da ya dakatar da aikin da yake yi, har sai zuwa lokacin da shugaba Muhammadu Buhari yace ya koma bakin aiki.

KU KARANTA: CJN ya bayyana yadda aka yi wasa da takardun sa a CCT

Tun a 2017 ne Yemi Osinbajo ya nemi Obono-Obla ya daga kafa na zuwa wani lokaci. Daga baya kuma Mataimakin shugaban kasar yayi ta aikawa Obla gargadi cewa ya takaita aikin da yake yi, amma yayi murisi kamar ba ayi ba.

Osinbajo ya fara rubutawa wannan kwamiti takarda ne bayan da ya ga Mista Obono-Obla da mutanen sa sun fara sakin layi daga aikin da aka sa su. A karshen 2017 ne aka tuntubi Ministan shari’a yana nema a ja kunnen kwamitin.

Ade Ipaye wanda shi ne mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ya aika takarda ga Minista Abubakar Malami domin a dawo da wannan kwamiti na SPIP kan hanya, amma hakan bai ci tura ba duk da wasikun da aka aika masa.

KU KARANTA: INEC ta hana Okorocha takardar nasara bayan ya ci zaben Sanata

Daga cikin abin da aka fadawa shugaban kwamitin shi ne ya daina amfani da sunan fadar shugaban kasa, kuma ya rika bin doka wajen binciken wadanda ake zargi. Okoi Obla ya maidawa Osinbajo martani cewa zai gyara amma bai yi hakan ba.

Ministan shari’a na Najeriya ya karbi korafi iri-iri a kan wannan Hadimi na shugaban kasa, amma har yau bai shiga taitayin sa ba. A karshe dai Yemi Osinbajo ya umarce sa da ya dakata da aikin da yake yi amma har gobe bai fasa ba.

Sauran ‘ya ‘yan wannan kwamiti da aka nada Okoi Obla ya shugabanta dai ba su ma san abin da ke faruwa ba, saboda ware su da aka yi. Obla ya kuma hakikance a kan cewa aikin sa yake yi kamar yadda shugaban kasa da kan sa ya sa shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel