Hukumar DSS ta tura ma Buhari sabon babban dogari

Hukumar DSS ta tura ma Buhari sabon babban dogari

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta tura ma shugaban kasa Muhammadu Buhari sabon babban dogarin da zai bashi tsaro, Idris Kassim Ahmed, wanda tuni ya fara aiki babu kama hannun yaro, biyo bayan tafiyar tsohon dogarin shugaban kasan.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an hangi sabon dogarin, Idris Kassim a fadar shugaban kasa a ranar Juma’a yayin da yake gadin Buhari a lokacin da ake gudanar da sallar Juma’ah, da kuma bayan kammala sallar.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta lashe kujeru 14 na majalisar dokokin jahar Nassarawa

Hukumar DSS ta tura ma Buhari sabon babban dogari
Bashir dauke da riga a hannu
Asali: UGC

Idris ya maye gurbin tsohon dogarin Buharinne, Bashir Abubakar, wanda Buhari ya zabeshi a matsayin dogarinsa bayan cin amanar da tsohon dogarinsa Abdulrahman Mani yayi masa, wanda hakan yasa aka sallameshi daga aiki gaba daya.

Majiyoyi sun ruwaito Bashir Abubakar, wanda kafin nadinsa dogarin shugaban kasa shine mataimakin daraktan hukumar DSS reshen jahar Bayelsa, an turashi yin kwas ne a jami’ar Buenos Aires dake kasar Ajantina, kuma a ranar Alhamis yayi aikinsa na karshe a Villa.

Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa shugaban hukumar DSS, Yusuf Bichi ne ya nemi a shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cire Bashir saboda wasu dalilai da basu bayyana ba har zuwa yanzu.

Daga karshe majiyarmu ta ruwaito ana sa ran hukumar DSS zata fitar da sanarwa game da nadin sabon babban dogarin shugaban kasan, tare da sanar da cire tsohon dogarin daga mukamin da yayi dare dare akai tun daga shekarar 2015.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel