Jerin gwarazan daliban da zasu wakilci Najeriya a gasar haddar Qur’ani ta duniya
An sanar da jerin sunayen zakakuran daliban Najeriya kuma mahaddata Al-Qur’ani da zasu wakilci Najeriya a gasar haddar Qur’ani ta duniya gaba daya da zata gudana a kasar Turkiyya, a watan Mayun shekarar 2019.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin wadanda zasu wakilci Najeriya a fannin Maza akwai Alaramma Abdurrahman Bunu daga jahar Bornu, da kuma Yusuf Yahaya daga jahar Edo, dukkaninsu sun ciri tuta wajen rera karatun Qur’ani da tajwidi.
KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta lashe kujeru 14 na majalisar dokokin jahar Nassarawa
Kungiyar cigaban Musulunci ta Najeriya, IPIN tare da hadin gwiwar gidauniyar Diyanet ta kasar Turkiyya ce suka shirya gasar sharan fagge a Najeriya, wanda ya gudana a babban Masallaci dake babban birnin tarayya Abuja, daga nan aka zabi wadanda zasu wakilci Najeriya.
Sakamakon gasar da aka kammala a Abuja ya nuna Alaramma Bunu ne yazo na daya a haddar izu sittin, yayin da Ismail Umar daga jahar Neja, da Abdulmalik Ahmad daga jahar Ogun suke bi masa.
Haka kuma Malam Yahaya yazo na daya a haddar Tangeemi, yayin da Ibrahim daga jahar Borno, da Ajmul Nura Shema daga jahar Katsina suka rufa masa baya a matsayin na biyu da na uku.
A bangaren Mata kuwa, Maimuna Abdurrahman daga Abaji ce ta zama zakakura a haddar izu 5, yayin da Aisha Sani daga Kuje ta lashe gasan haddar izu 10, Fauziyya Shehu daga AMC ta lashe haddar izu 20, Halima Muhammad Gwagwalada ta lashe izu 40, sai Surayya Muhammad ta lashe izu 60.
Dayake nasa jawabin, shugaban IPIN, Dakta Muhammad Kabir Adam ya bayyana cewa sun fara shirya gasar ne a shekaru hudu da suka gabata don karfafa ma daliban ilimi haddan Al-Qur’ani da sauti mai dadi da kuma tajwidi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng