‘Yan bindiga sun kai hari Filato: Sun kasha shanu 81, sun sace 32

‘Yan bindiga sun kai hari Filato: Sun kasha shanu 81, sun sace 32

Shugabannin kungiyar makiyaya a jihar Filato; ‘Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) da ‘Fulani Youth Association of Nigeria (FYAN)’ su yi zargin cewar wasu ‘yan bindiga sun kashe shanu 81 tare da sace wasu 32 a wani hari da suka kai kusa da wata makaranta a Kwall dake hukmar Bassa a jihar Filato.

MACBAN da FYAN sun bayyana cewar babu wani dalilin kai harin a kan mutanensu.

Muhammad Nura Abdullahi, shugaban kungiyar MACBAN a jihar Filato, ya shaidawa manema labarai cewar ‘yan bindigar sun harbe shanu 81 yayin da suka kashu wasu ta hanyar caccaka masu adda. Sannan ya kara da cewa sun sace shanu 32 tare da raunata 48 da aka garzaya da su zuwa kwata don gudun sake yin asarar su.

Abdullahi ya kara da cewa sun sanar da rundunar soji ta ‘operation safe haven (OPSH)’ da kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato, Isaac Akinmoyede, a kan harin kuma sun turo wakilai domin daukan kididdigar barnar da ‘yan bindigar suka tafka.

‘Yan bindiga sun kai hari Filato: Sun kasha shanu 81, sun sace 32
‘Yan bindiga sun kai hari Filato: Sun kasha shanu 81, sun sace 32
Asali: UGC

‘Yan bindiga sun kai hari Filato: Sun kasha shanu 81, sun sace 32
‘Yan bindiga kashe shanu 81, sun sace 32
Asali: Twitter

‘Yan bindiga sun kai hari Filato: Sun kasha shanu 81, sun sace 32
‘Yan bindiga sun kasha shanu 81
Asali: Twitter

Rundunar sojin OPSH ta san da maganar kai harin sannan na kwamishinan ‘yan sanda da kai na kuma bisa shawara sa na sanar da DPO na yankin. Kwamanda da DPO sun ziyarci wurin da ‘yan bindigar suka kai harin,” a cewar Abdullahi.

Shi kuwa Saeedu Maikano na FYAN cewa ya yi an kai harin ne da gan-gan domin tunzura makiyayan tare da bayyana mamakinsa a kan yadda har yanzu gwamnatin jihar Filato ba ta fitar da jawabin Alla-wadai da kai harin ba.

DUBA WANNAN: Kisan mutane 30 a Kaduna: Buhari ya bawa ma su kai hari shawara

A cewar Maikano; “yanzu gwamnati na nufin Kenan ba zata iya kare mu da dukiyoyin mu ba? Shin sun san tsawon lokacin da ake dauka kafin a raini Saniya daya har ta girma? Da gan-gan aka kai wannan harin kuma babu wata niyya a wurin gwamnati na ba mu kariya.”

Tyopev Terna, kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Filato ya ki yarda ya ce komai a kan harin duk da manema sun nemi ya yi Karin bayani a kan hakan.

Manjo Adam Umar na OPSH ya tabbatar da kai harin tare da bayyana cewar ‘yan bindigar sun kada shanun zuwa daji kafin daga bisani su harbe su.

Sai dai y ace ba zai tabbatar da adadin shanun da aka kashe ko aka sace ba don a halin yanzu suna kokarin gano su waye wadanda su ka kai harin, kuma tuni an bi sahun su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel