Rashin samun dama da lokacin nutsuwa ya hana mu ba Atiku damar bincikar kayan zabe - INEC

Rashin samun dama da lokacin nutsuwa ya hana mu ba Atiku damar bincikar kayan zabe - INEC

Cikin wani sakon mayar da martani ga jam'iyyar PDP da kuma dan takarar ta na kujerar shugaban kasa, Atiku Abubakar, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC ta fayyace dalilai da kawowa yanzu ta gaza ba su damar gudanar da bincike kan Kayan zabe.

Biyo bayan kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar fiye da makonni biyu da suka gabata, Atiku Abubakar, dan takarar kujerar shugaban kasa da kuma jam'iyyar sa ta PDP, sun samu sahalewar kotun daukaka kara na umartar hukumar INEC akan ba su damar gudanar da bincike kan kayayyakin zabe da ta ribata yayin babban zaben kasa.

Shugaban hukumar INEC; Farfesa Mahmood Yakubu
Shugaban hukumar INEC; Farfesa Mahmood Yakubu
Asali: Twitter

Atiku da jam'iyyar PDP na ci gaba da kalubalantar sakamakon zaben kasa da zargin cewa an tafka magudi gami da rashin gaskiya yayin gudanar sa wajen rinjayar da nasara ga jam'iyyar mai ci ta APC a sanadiyar alfarma ta riko da akalar jagorancin kasar nan.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kawowa yanzu bayan tsawon makonni biyu da umarnin Kotu, hukumar zabe ta kasa ta gaza bai wa Atiku da jam'iyyar sa ta PDP damar gudanar da bincike akan kayayyakin zabe domin tattara shaidu da hujjoji gami da dalilai na kalubalantar zabe.

Yayin zayyana dalilai na rashin yiwa umarnin kotu da'a cikin gaggawa, hukumar INEC ta ce ta gaza samun sukuni da nutsuwar biyan bukatar Atiku a sakamakon bigewa wajen fuskantar harkokin zaben 'yan majalisun tarayya, gwamnoni da kuma 'yan majalisun dokoki na jiha.

KARANTA KUMA: Hukumar sojin kasa ta yiwa manyan dakaru sauye-sauyen aiki

Rotimi Oyekanmi, mai magana da yawun shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Mahmoud Yakubu, shi ne ya bayar da shaidar hakan yayin ganawar sa da maneman labarai na jaridar The Cable a garin Abuja.

Sai dai Mista Oyekanmi ya ce, Atiku da jam'iyyar PDP su sha kurumin su domin kuwa nan ba da jimawa ba hukumar INEC za ta biya bukatar su bisa ga tanadi na hukunce-hukunce da kuma tsare-tsaren ta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel