Har yanzu Alaranma Ahmad Sulaiman Ibrahim yana tsare

Har yanzu Alaranma Ahmad Sulaiman Ibrahim yana tsare

Mun ji labari cewa wadanda su kayi garkuwa da babban Alaranman nan na kungiyar Izala, Sheikh Ahmad Sulaiman Ibrahim sun kira Iyalin sa a waya. Jaridar Daily Trust ce ta rahoto wannan dazu.

Wani yaron Malamin addinin mai suna Malam Muhammad Nasir Dan-Kurna, shi ne ya bayyanawa manema labarai wannan. Muhammad Nasir Dan-Kurna yace wadanda su ka sace Malamin sun ta kiran Iyalin Malamin a waya.

Jaridar tace wadannan mutane da su ka sace Malamin sun kira Iyalin na sa har kusan sau 5 ta wayar salula, inda har aka ba Malamin daba ya zanta da Mutanen gidan na sa tun Ranar Juma’a da safe har zuwa yammacin Ranar.

Sai dai har yanzu babu bayani game da kudin da wadannan masu garkuwa da mutane su k enema kafin su saki Alaranman. Nasir Dan-Kurna yace bai san ko an bukaci kudi ba, amma ya ba wani Alaranma lambar wadannan Miyagu.

KU KARANTA: 'Dan Najeriya ne wanda yake jan sallah a Masallacin da aka hallaka mutum 40

Bayan wadannan mutane da su ka sace Alaranman, sun kira mutanen sa a waya, an karbi lambar su, an ba Alaranma Nasiru Gwandu. Yanzu dai masu garkuwa da mutanen su na tattaunawa da Takwaran sa Alaranma Gwanzu.

Wannan yaro na Alaranman ya tabbatar da cewa Nasiru Gwandu da wadannan mutane da su kayi ram da Mai gidan na sa, su na can su na tattaunawa inda ake kokarin cin ma matsaya, amma yace bai san nawa su ke nema ba.

Iyalin wannan babban Malami ya da ya saba jan baki a kan mimbarin kungiyar Izala sun godewa gudumuwar da jama’a su ke ba su inda su ka nemi a cigaba da kwarara addu’a har a sake sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel